An Zabi Gwarzuwar ‘Yar Wasa na Gasar Firimiyar lig na Mata NWFL 2025/26 Makon Farko.
An zabi Janet Akekoromowei, ‘yar wasan gaba ta Bayelsa Queens a matsayin gwarzuwar ‘yar wasa a gasar Firimiyar lig na Mata NWFL, ta Najeriya.
Janet ta samu kuri’u 1209, inda ta doke ‘yar wasan tsakiya ta Nasarawa Amazons, Hembafan Ayatsea wacce ta samu kuri’u (754) a matsayi na biyu, mai tsaron gida na Robo Queens, Olaide Olawale ta tashi da kuri’u (682).
Nasarar ta samune a babban rawar da Akekoromowei ta taka a wasan mako farko wa ƙungiyar kwallon kafa Mata na Bayelsa Queens, inda ta nuna kwazo, daidaito, da kuma jagoranci nasara a wasa yayin da gasar Premiership ta fara kakar wasa ta 2025/26.
Kokarin ‘yar wasa Janet, da tayi ba wai kawai ya jawo mata haskakawa ba, har ma ya nuna niyyar Bayelsa Queens a matsayin wadanda suka shirya fafatawa a gasar farko.
Inda al’uma suka taya ‘yar wasa Janet murna kan wannan kyauta da kuma fatan samun nasara a wasannin na gaba.


