Gwamnonin Arewacin Najeriya, sun kaddamar da Asusun tsaro a yankin, Inda kowacce jiha za ta ba da Biliyan ɗaya duk wata.
Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya tare da sarakunan gargajiya sun sanar da kafa Asusun tsaro na yankin Arewa, wanda kowace jiha da kananan hukumomin ta za su riƙa ba da naira biliyan ɗaya a duk wata domin magance matsanancin tsaro a yankin.
Sanarwa mai dauke da sa hannun Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, Gwamnan jihar Gombe, kuma shugaban kungiyar Gwamnonin Arewa ta bayyana cewa, wannan na cikin muhimman matsaloli da aka cimma a ƙarshen taron haɗin gwiwar Kungiyar Gwamnonin Arewa da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewacin Najeriya, da aka gudanar a ranar Litinin a gidan Sir Kashim Ibrahim dake Kaduna.
Taron ya samu halartar dukkan gwamnonin jihohin Arewa guda goma sha tara (19) da shugabannin majalisun gargajiya na kowacce jiha.
A yayin taron an tattauna kan manyan batutuwa da suka shafi yankin da Najeriya baki ɗaya, inda aka yanke waɗannan muhimman shawarwari.
Gaisuwar ta’aziyya ga jihohin da hare hare suka shafa. Gwamnonin sun yi jaje ga gwamnatoci da al’ummomin Kebbi, Kwara, Kogi, Neja, Sakkwato, Jigawa da Kano bisa kashe-kashe da sace sacen ‘yan makaranta da al’umma da aka yi a kwanakin baya haka kuma an miƙa ta’aziyya ga waɗanda hare-haren Boko Haram suka rutsa da su a Borno da Yobe.
Dakatar da hakar ma’adanai na wucin gadi:
Gwamnonin sun nuna damuwa kan yadda hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba ke kara haifar da matsalolin tsaro a Arewacin kasar a saboda haka sun bukaci shugaban ƙasa ya umarci Ministan Ma’adanai ya dakatar da dukkan hakar ma’adanai na watanni shida, domin gudanar da cikakken bincike da tantance lasisin hako ma’adanai tare da hadin gwiwar gwamnonin jihohi.
Kafa Asusun Tsaro na Yanki:
A wani muhimmin mataki, kungiyar ta amince da kafa asusun tsaro na Yankin Arewa, wanda za a rika ba da naira biliyan ɗaya daga kowace jiha da kananan hukumomi duk wata, domin sauƙaƙa yaki da kalubalen tsaro.
Sannan tattaunawar ta amince a sake gudanar da wani taro a wani lokaci da za a sanar nan gaba.


