Cambvodia ta ce sojoji da jiragen yakin kasar thailand suna ci gaba da kai hare-hare a wasu yankunan bakin iyakarsu a ranar asabar da safe, sa’o’i bayan da shugaba Donald Trump na Amurka yayi ikirarin cewa ya kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakanin makwabtan biyu.
Ma’aikatar yada labarai ta Cambodia ta ce sojojin Thailand ba su daina kai hare-haren kan cibiyoyin Cambodia ba.
Rundunar sojojin Thailand ta mayarda martani da cewa Cambodia tana ci gaba da keta dokoki na kasa da kasa ta hanyar auna hare-hare a kan cibiyoyin fararen hula tare da dasa nakiyoyi.
Shugaba Trump yace Thailand da Cambodia sun yarda zasu tsagaita bude wuta daga jiya jumma’a a bayan tattaunawar da yayi ta wayar tarho da firayim ministan Thailand Anutuin Charnvirakul da firimiyan Cambodia Hun Manet.
Sai dai kuma babu daya daga cikinsu da yayi maganar cewa an cimma wata yarjejeniya a bayanan da suka yi bayan tattaunawa da shugaban na Amurka, har ma firayim ministan Thailand din yace babu wata tsagaita wutar da aka cimma.
A cikin wata sanarwar da ya fitar ranar asabar a shafin Facebook, firimiyan Cambodia Manet yayi nuni da wayar da suka yi da shugaba trump da tattaunawar da suka yi tun da fari da firayim ministan Malaysia Anwar Ibrahim, yana mai fadin cewa kasarsa tana ci gaba da neman hanyar warware rikicin bakin iyakar cikin lumana.


