Tun fiye da shekaru sittin da mafi yawan kasashen Afirka suka sami ‘yancin kai, masana sun bayyana cewa har yanzu nahiyar na fama da tsarin mulkin mallaka da rashin samun ‘yanci a fannoni daban-daban na rayuwa.
A wani taro da masana daga kasashen duniya suka halarta, da masu fafutukar ‘yanci da hukumomi da dalibai daga kasashe daban-daban na Afirka, wadanda suka taru a Jami’ar Jos, an gabatar da kasidu da suka yi nazari kan makomar Nahiyar Afirka da hanyoyin samar da mafita.

Taron na tunawa da wani matubuci da fafutuka, Frantz Fanon da yayi rubuce-rubuce da suka zame kamar wahayi kan makomar nahiyar Afirka a fannonin damokradiyya, gazawar shugabanci da sauransu.
Malam Jibrin Ibrahim na cibiyar damokradiyya da ci gaba dake Abuja, Najeriya, yace taron yayi nazari ne kan rashin tasiri da ‘yancin kai a Afirka ya kasance.
Shima Malam Yunusa Zakari-Ya’u na cibiyar fasahar sadarwa da ci gaba dake Kano, Najeriya, yace yawan juyin mulki da ake samu a wassu kasahen Afirka, saboda rashin adalcin shugabanni ne.

Komared Sam Magaji, malami a Jami’ar Jos, yace suna horadda dalibai su san yadda shugabanni a baya suka yi mulki, da yadda daliban zasu yi nazarin abubuwan dake faruwa yanzu, da yadda za’a yi gyara nan gaba.
Mr Charles Toheyo, malami a Jami’ar Nkerere dake kasar Uganda, yace idan har shugabannan dake mulki basu sauya tunaninsu ta yadda zasu kyautata wa al’umma ba, to ba shakka za’a ci gaba da zaman tankiya.
Adam Khalid, dalibi a Jami’ar Jos, yace matasa a Afirka a shirye suke su kawo sauyi, sai dai har yanzu basu sami jagoranci daga dattawa ba, saboda dattawan kansu kadai suka sani.

A taron na wuni biyu, an gabatar da kasidu kimanin saba’in, da suka kunshi samarda mafita kan matsalolin da suka hana kasashen Afirka samun walwala da ci gaba.


