Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cewa Najeriya za ta karɓi bakuncin taron Investopia tare da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) a birnin Legas a watan Fabrairu mai zuwa, domin jawo hankalin masu zuba jari daga sassa daban-daban na duniya.

Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a yayin taron Abu Dhabi Sustainability Week (ADSW) na shekarar 2026, inda ya ce shirin zai taimaka wajen bunƙasa jarin da zai tallafa wa ci gaban tattalin arziki mai dorewa.
A gefen taron, Najeriya da UAE sun kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar tattalin arziki ta CEPA, wadda ke da nufin zurfafa haɗin gwiwa a fannonin kasuwanci, makamashi, gine-gine, sufurin kayayyaki da kasuwancin zamani na intanet.
Shugaban UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, tare da ministocin kasashen biyu, sun halarci sanya hannun kan yarjejeniyar da Tinubu ya bayyana a matsayin tarihi da dabarar bunkasa dangantakar kasashen biyu.

Tinubu ya bayyana cewa Investopia zai haɗa masu zuba jari, ‘yan kasuwa, masu kirkire-kirkire da masu tsara manufofi domin mayar da ra’ayoyi zuwa jarin da zai amfani al’umma, sannan ya ce Najeriya na da burin tara kusan dala biliyan 30 a duk shekara domin ayyukan sauyin yanayi da masana’antu masu kare muhalli, yana mai jaddada bukatar sauya tsarin hada-hadar kuɗin duniya domin sauƙaƙa wa ƙasashe masu tasowa samun jari ba tare da nauyin bashi ba.
Shugaban ƙasar ya kuma yi nuni da gyare-gyaren makamashi da tattalin arziki da gwamnatinsa ke aiwatarwa, ciki har da Dokar Lantarki ta 2023 da kuma manufofin kasuwar carbon, yana cewa hakan ya ƙara amincewar masu zuba jari.
Ya ƙara da cewa fitar da kayayyakin da ba na mai ba ya ƙaru da kashi 21 cikin 100, tare da alkawarin cewa Najeriya a shirye take ta yi aiki da abokan hulɗa domin gina ci gaba mai ɗorewa, adalci da amfani ga kowa.


