Hukumomi a jamhuriyar Nijar sun umurci jami’an fiton kaya (Douanes) da su tsaurara binciken kayan da ke shigowa kasar daga Najeriya. Matakin wanda ke da nasaba da dalilan tsaro, wanda a ‘yan kwanaki kadan da suka shige aka samu tarin wasu ababe masu fashewa a wata motar jigila da ta tsallaka Nijar daga wata kasar waje. Tuni ‘yan kasuwa da kungiyoyin fararen hula suka fara bayyana matsayinsu a kai.
Ta hanyar wata takardar da ya aike wa mukarrabansa na illahrin jihohi ne shugaban hukumar Douanes na kasa Kanal Mohamed Yacouba Siddo ya umurce su da kara zuba ido kan kayayakin da ke shiga Nijar ta iyakar ta da Najeriya, abinda ke nufin daga yanzu za a sauke kayayakin da matakin ya shafa domin yi masu dai dai kafin samun izinin tsallakowa Nijar.
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Import Export Alhaji Yacouba Dan Maradi ya ce, matakin wanda a ka ayyana cewa abu ne da ke da nasaba da harakokin tsaro na zuwa ne a wani lokacin da alamu ke nuna yadda barazanar tsaro ke kara fadada a kasashen sahel da na yammacin Afirka, A ra’ayin shugaban kungiyar ci gaban karkara da birane Alhaji Ali Kalla matakin ya zo a kan gaba.
Koda yake a na danganta abin da yanayin tsaro wasu daga cikin mazauna garuruwan iyakar kasashen biyu na da fargaba game da yadda za a tafiyar da shi.
Iyakar Nijar da Najeriya mai tsawon kilo mita sama da 1500 na matsayin iyaka mafi mahimmanci ga kowacce daga cikinsu, kasancewarta gimshiki a harakokin tattalin arziki da cudanyar al’umomin kasashen biyu. jihohi a kalla 5 na Nijar ne ke makwaftaka da jihohi 7 na arewacin Najeriya.
TSAURARA BINCIKE A IYAKAR NIJAR NAJERIYA


