Shugaba Bola Tinubu ya bukaci Majalisar Dokoki ta Kasa da ta fara aiki nan take kan kafa rundunar ‘yan sandan jihohi, lamarin da ya kai batun gyaran kundin tsarin mulki zuwa wani muhimmin mataki.
Kudirin Kafa ‘Yan Sandan Jihohi na daga cikin kudirori 44 da ke gaban Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai, kuma ana sa ran za a kada kuri’a a kansu a wannan makon.
Idan sun tsallake Majalisar Tarayya, dole ne akalla kashi biyu bisa uku na Majalisun Dokokin Jihohi su amince kafin shugaban kasa ya sanya hannu su zama doka.
Masu sharhi na ganin yiwuwar kudirin ya zama doka, sakamakon tabarbarewar tsaro da kuma goyon bayan da Tinubu da gwamnonin jihohi da dama ke nunawa ga kafa ‘yan sandan jihohi


