An kiyasta asarar kasafin kudi na shekara 2026 na ma’aunin tattalin arziki na cikin gida a Nigeria zai kai kashi 4.28 cikin dari, yayin da shugaba Bola Tinubu ya gabatar da kasafin kudi na naira tiriliyan 58, da biliyan 18, da niyyar karfafa gyare-gyaren tattalin arziki, da kuma bunkasa ci gaban kasa.
Shugaba Tinubu ya ce asarar ta kai kimanin naira tiriliyan 23, da biliyan 85, a lokacin da yake yiwa ‘yan majalisa bayani kan kasafin kudin ranar Jumu’a.
Kasafin kudin dai ya ware naira tiriliyan 15 da biliyan 52 don biyan bashi, yayin da kuma aka ware Naira tiriliyan 26 da biliyan 8 don manyan ayyuka da suka hada da tsaro, ayyukan gini, ilimi da kuma lafiya.


