Rundunar sojojin bani Isra’ila ta ce ta kashe wani babban kwamandan Hamas mai suna Raed Saed, a harin da ta kai kan wata mota ranar asabar a birnin Gaza.
Wannan shine kisa na wani babban dan kungiyar Hamas na farko tun lokacin da aka kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Oktoba.
A wata sanarwar hadin guiwa, firaminista Benjamin Netanyahu da ministan tsaron kasar sunce an kai hari a kan Saed ne a bayan wani harin da Hamas ta kai da nakiya ta raunata wasu sojojin Isra’ila biyu ranar asabar.
Hukumomin kiwon lafiya a Gaza sun ce harin da Isra’ila ta kai kan motar a birnin gaza ya kashe mutane biyar, ya raunata wasu akalla 25. Amma ba a ji daga bakin kungiyar Hamas ko ma’aikatan kiwon lafiya a kan ko akwai Saed a cikin wadanda aka kashe ba ya zuwa yanzu.
A cikin wata sanarwar da ta bayar, hamas tayi Allah wadarai da wannan harin a zaman wanda ya keta yarjejeniyar tsagaita wuta, amma ba ta tabbatar da ko akwai Saed a cikin wadanda aka kashe ba, haka kuma ba ta yi barazanar daukar fansa ba.


