Al’ummar Arewa a Jihar Inugu na ci gaba da yin sam-barka tare da bayyana farin ciki da bude sabon gidan damben gargajiya da aka yi a Inugu babban birnin jihar bayan shafe shekaru da wasan ya dauke.
Mai gidan damben Cif Emeka Nnolim, wani dan kabilar Igbo ya ce, “Wannan hanya ce ta hada kawunan kabilu daban-daban na Najeriya don karfafa zumunci ta hanyar raya wasan dambe a tsakanin matasan Arewa da ke wannan jihar da wadanda suke nesa. Wannan matakin farko ne na bunkasa wasannin gargajiya a Jihar Inugu don mayar da jihar cibiyar wasannin gargajiya a Najeriya.”
Bayan kammala bude filin wasan, shugaban al’ummar Arewa a jihar da kuma babban mai taimaka wa gwamnan Jihar Inugu kan ayyuka na musamman, Alhaji Abubakar Yusuf Sambo ya tofa albarkacin bakinsa kan dawowar wasan dambe a jihar.
“Na yi farin ciki da ganin cewa da duk da cewa muna kudancin Najeriya muna tuna abin da aka san Arewa da shi watau wasan dambe. Wasa ne na hada zumunci, kuma duk inda ake irin wannan zamu bada goyon baya,” inji Alhaji Yusuf Sambo.

A cewar wani dan dambe dan asalin garin Hadejia na Jihar Jigawa mai suna Adamu wanda aka fi sani da Shagon Baturiya, “Wasa ya yi dadi yadda ake so. Sabon gidan dambe da aka bude anan Inugu ya yi kyau. Na yi farin ciki kuwa,” a yayin da wani shahararren dan wasa Badaman Bauchi, shi ma cike da farin ciki, ya mika goron gayyata zuwa daukacin ‘yan wasa da cewa:
“Filin sabon gidan wasan dambe da aka bude a Inugu ba laifi. Toh domin haka, muna kira ga sauran ‘yan wasa da suke nesa da su zo. Muna gayyatar kowa da kowa su zo.”
An bude gidan damben ne unguwar Emene wacce take cikin birnin Inugun, inda matasan Arewa sun fara tururuwa don nishadantar da kansu da take taken ‘yan wasa da kide-kiden gargajiya masu faranta ran gaske.


