Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata Afrika
  • NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa Afrika
  • Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno Amurka
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe Afrika
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya Afrika

Wasan Dambe Ya Dau Sabon Salo A Jihar Inugu
Published: December 19, 2025 at 2:56 PM | By: Yusuf Aliyu Harande

Al’ummar Arewa a Jihar Inugu na ci gaba da yin sam-barka tare da bayyana farin ciki da bude sabon gidan damben gargajiya da aka yi a Inugu babban birnin jihar bayan shafe shekaru da wasan ya dauke.

Mai gidan damben Cif Emeka Nnolim, wani dan kabilar Igbo ya ce, “Wannan hanya ce ta hada kawunan kabilu daban-daban na Najeriya don karfafa zumunci ta hanyar raya wasan dambe a tsakanin matasan Arewa da ke wannan jihar da wadanda suke nesa. Wannan matakin farko ne na bunkasa wasannin gargajiya a Jihar Inugu don mayar da jihar cibiyar wasannin gargajiya a Najeriya.”

Bayan kammala bude filin wasan, shugaban al’ummar Arewa a jihar da kuma babban mai taimaka wa gwamnan Jihar Inugu kan ayyuka na musamman, Alhaji Abubakar Yusuf Sambo ya tofa albarkacin bakinsa kan dawowar wasan dambe a jihar.

“Na yi farin ciki da ganin cewa da duk da cewa muna kudancin Najeriya muna tuna abin da aka san Arewa da shi watau wasan dambe. Wasa ne na hada zumunci, kuma duk inda ake irin wannan zamu bada goyon baya,” inji Alhaji Yusuf Sambo.

A cewar wani dan dambe dan asalin garin Hadejia na Jihar Jigawa mai suna Adamu wanda aka fi sani da Shagon Baturiya, “Wasa ya yi dadi yadda ake so. Sabon gidan dambe da aka bude anan Inugu ya yi kyau. Na yi farin ciki kuwa,” a yayin da wani shahararren dan wasa Badaman Bauchi, shi ma cike da farin ciki, ya mika goron gayyata zuwa daukacin ‘yan wasa da cewa:

“Filin sabon gidan wasan dambe da aka bude a Inugu ba laifi. Toh domin haka, muna kira ga sauran ‘yan wasa da suke nesa da su zo. Muna gayyatar kowa da kowa su zo.”

An bude gidan damben ne unguwar Emene wacce take cikin birnin Inugun, inda matasan Arewa sun fara tururuwa don nishadantar da kansu da take taken ‘yan wasa da kide-kiden gargajiya masu faranta ran gaske.

Wasanni

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Sanda Sunce Mutum Daya Ne Yakai Hare-Haren Jami’ar Brown Da Kuma Na MIT Boston
Next Post: Shugaba Tinubu Ya Gabatar da Kasafin Kuɗin 2026

Karin Labarai Masu Alaka

Alhassan Yayi Nasarar Kifar Da Wurkilili A Gasar Damben Gargajiya Wasanni
Bana Ba Harka Ga ‘Yan-Wasan Kwallon Kafar Najeriya Wasanni
Liverpool Tayi Rashin Nasara A Wasanni Tara Wasanni
Hawan Durba A Fadar Sarkin Zazzau Afrika
Shugaban Hukumar Kwallon Kafa Ta Senegal Yaki Amincewa Da Hukuncin CFA Afrika
Da Alamu Ronaldo Zai Buga Dukkan Wasanni Da Gasar Kofin Duniya A 2026 Wasanni

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata
  • NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa
  • Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • APC Ta Sauya Jerin ‘Yan Takararta Bayan Nazarin Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Fidda Gwani Afrika
  • Boko Haram Sun Farmaki Sansanin Sojoji A Borno Tsaro
  • Kasashen Turai: Bazamu Yarda Da Dokar Harajin Trump Ba Labarai
  • Maganganun Jami’an Shige Da Fice Dana Shugaban Kasa Trump Suna Cin Karo Da Juna Amurka
  • Hafsan Sojin Najeriya: Samar Da Sabbin Wajen Horas Da Sojoji Zai Inganta Tsaro Tsaro
  • Gwamnan Neja Bago Na Cin Zarafin Talakawan Da Suka Zabe Shi Labarai
  • Amurkawa Suna Turuwa Zuwa Kasar Faransa Duk Da Rashin Jituwa A Tsakanin Kasashen Amurka
  • Sakataren Gwamnatin Amurka Ya Bayyana Bawa Kungiyoyin Agaji Damar Kai Taimako Sudan Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.