Yaki tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran ya shiga kwana na biyar. Ana ci gaba da musayar wuta. A jiya Amurka ta nutsar da jirgin ruwan yakin Iran a wajajen kogin Srilanka. Iran kuma na gab da zabar wanda zai maye gurbin Ayatollah Ali Khameni, wanda ake sa ran dan sa Mojtaba ne zai gaje shi.
Shugaban kasar Amurka da masu bashi shawara sun fara tattaunawa game da rawar da Amurka bayan yakin a cewar fadar White House.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila da Amurka suka kaiwa Iran, da kuma harin da ita Iran din ta kai na ramuwa a yankunan Gabas ta tsakiya, inda tace abun ya sabawa dokokin majalisar.
A wani labarin kuma, Isra’iala ta gargadi mazauna yankunan kudancin Lebanon da suyi gaggawar barin wajen ranar Laraba, inda ta umurce su da su koma arewacin kogin Litani. Isra’ila ta kaiwa kasar Lebanon hari tun bayan da mayakan Hezbollah suka shiga yakin a bayan Iran. Hezbollah ta kaiwa Isra’ial hari da jiragen drone da bama bamai ranar Litinin.
A wajen jiragen dakon man fetur na Gabas ta tsakiya kuma, har yanzu suna tsaye waje daya ba damar wucewa ta hanyar mashigin ruwa na Hormuz da Iran ta rufe. A kalla jiragen ruwa 200 wanda suka hada da masu dakon man fetur da iskar gas, har ma da kaya suka samu tsaiko sakamakon yakin da ake tafkawa.


