Najeriya ta yi asarar kusan naira tiriliyan 1 wajen fitar da kaya bayan harajin Trump
Fitar da kayayyakin Najeriya zuwa Amurka ya ragu da naira biliyan 940.98 a cikin watanni tara na farkon shekarar 2025, yayin da shigo da kaya daga Amurka ya tashi zuwa naira tiriliyan 6.80, lamarin da ya jefa Najeriya cikin gibin cinikayya na kusan naira tiriliyan 3.15.
Bayanin Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) sun nuna cewa fitar da kaya ya ragu daga naira tiriliyan 4.59 a 2024 zuwa naira tiriliyan 3.65 a 2025, yayin da shigo da kaya ya ƙaru da sama da kashi 125 cikin 100.
Tabarbarewar cinikayyar ta zo ne bayan Amurka ta ƙara harajin kayayyakin Najeriya daga kashi 14 zuwa 15 cikin 100 a ƙarƙashin tsarin harajin “reciprocal”, wanda ya fi shafar kayayyakin da ba na man fetur ba.
Sakamakon haka, Amurka ta fita daga cikin manyan ƙasashen da Najeriya ta fi fitarwa kaya zuwa gare su a zango na biyu da na uku na 2025, duk da cewa har yanzu tana daga cikin manyan ƙasashen da Najeriya ta fi shigo da kaya daga gare su.


