Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Akwai Alamar Shawarwari Tsakanin Amurka Da Turai Zai Kawo Karshen Yakin Rasha
Published: December 23, 2025 at 9:16 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Ukraine Volodmyr Zelensky, ya fada ranar litinin cewa, shawarwari da aka gudanar da jami’an Amurka da turai, da zummar kawo karshen yakin kasar da Rasha da yanzu ya kusa cika shekaru hudu, akwai alamar zai haifar da da mai ido.

Wakilan Ukraine karkashin jagorancin wani babban jami’in kasar Rustem Umerov, tare da­ wakilai daga turai sun gudanar da shawarwari da jakadun Amurka na musamman ciki har da wadanda aka yi a baya bayan nan a Florida.

Haka nan shi ma wakilin Rasha Kirill Dmitriev, wanda jakadan shugaba Putin kan zuba jari, shima ya gudanar da shawarwari da jami’an Amurka a zaman da suka yi a jihar Florida.

Wakilan duka sassan biyu, sun fada ranar Litinin cewa za su koma gida domin sanar kasashen na su kan abubuwa da suka tattauna akai.

A bangaren Amurka kuma jakadan shugaba Trump Steve Witkoff, da surkin Trump Jared Kushner ne suka wakilci Washington.

A jawabin da ya sabawa yi wa al’ummar kasarsa a ko wani dare, shugaba Zelensky yace akwai bukatar a tsananta matsin lamba kan Rasha domin rage mata kwarin guiwar kaddamar da yake yake.

Amurka, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Asusun IMF Zai Bawa Kasar Misra Lamunin Sama Da Dala Biliyan 2
Next Post: Akwai Shakku Akan Sanin Wacce Kungiyar Kwallon Kaface Zata Lashe Gasar Kofin Afirka Da Akeyi A Morocco

Karin Labarai Masu Alaka

Za’a Fuskanci Bala’in Yunwa A Najeriya Labarai
Bayan Rikicin Manoma Da Makiyaya, Kwamitin White Paper Ya Ziyarci Bojude Da Kwami Afrika
Mamakon Ruwan Sama Da Iska Ya Hallaka Mutane Uku A Jihar Yobe Labarai
Shugaban Amurka Yayi Barazanar Kulle Wani Dan Jarida Amurka
3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
Mizanin Tattalin Arzikin Najeriya Na 2024 Ya Karu Da Kashi 3.84% Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kamfanonin Jiragen Sama Suna Fama Da Karin Farashin Mai Labarai
  • Paparoma Leo: Zai Kai Ziyara Ƙasar Angola Labarai
  • Muhawara Mai Zafi Tsakanin APC da ADC Shirye-Shirye
  • Amurka Zata Kamallah Yaki Da Iran A Makonni Biyu Masu Zuwa Amurka
  • Muhimmin Sako Ga Alhazai Dake Kasar Saudiya Afrika
  • Wasu Muhimman Abubuwa Da Najeriya Ba Zata Manta Da Su Ba A 2025 Labarai
  • Gwamna Fubara Ya Koma Jam’iyar APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sojojin Najeriya Sun Kwato Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.