Gwamnatin Venezuela tace ta saki karin mutane 88 wadanda ta tsare su bayan zanga zangar da ta biyo bayan zaben kasar da aka gudanar cikin watan yulin bara.
Wannan shine sake mutane masu yawa haka cikin ‘yan makonni, a dai dai lokacin da kasar take fuskantar karin matsin lamba daga Amurka kan gwamnatin shugaba Nicolas Maduro.
Wannan sakin mutane da gwamnatin tace tayi ranar daya ga watan nan na sabuwar shekara, biyo bayan sanarwa da gwamnatin ta bayar cewa ta saki mutane 99 ranar 26 ga watan Disamba, wanda ya kawo adadin wadanda gwamnatin tace ta saka zuwa 187.
Sai dai kungiyoyin rajin kare hakkin Bil’adama a kasar suna tababar yawan mutane da gwamnatin take ikirarin Cewa ta sake su.


