Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kaiwa masu zanga-zanga a Iran dauki idan jami’an tsaro suka yi harbi a kan su, kwanaki bayan hargitsin da yayi sanadiyyar kashe mutane da dama, wannan hargitsi na iya zama mafi girman barazana ta cikin gida ga hukumomin Iran.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafin sada zumunta, shugaba Trump ya ce sun shirya, kuma sun daura damara, ya kara da cewa Amurka ta tada bom a masana’antun nukiliya na Iran a watan Yuni, inda ta tallafawa harin da Isra’ila ta kaiwa kasar ta sama, don tarwatsa shirin ta na nukiliya da shugabannin sojojin ta.
Da yake martani ga Trump, babban jami’in Iran Ali Larjani ya yi gargadin cewa tsoma bakin Amurka a rikicin cikin gida na Iran zai iya haifar da tashin hankali a gaba daya gabas ta tsakiya kuma Iran na Goyon bayan sojojin wakilcin ta a Lebanon, Iraq da kuma Yemen.


