Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya wato (INEC) ta sake dawo da yin rajistar masu zaɓe na dindindin a faɗin Najeriya, inda hakan ke nuna fara zango na biyu na aikin.

INEC ta ce an dawo da aikin ne bayan kammala zangon farko da ya ƙare a ranar 10 ga Disamba, 2025.
Hukumar takara da cewa, sama da ’yan Najeriya miliyan 9.8 ne suka fara rajistar yanar gizo a zangon farko, yayin da kusan miliyan 2.57 ne aka kammala musu Rijistar gaba ɗaya.
Hukumar ta bayyana cewa an yi amfani da tazara tsakanin zango na biyu wajen gudanar da ayyukan doka, ciki har da nuna kundin masu zaɓe domin karɓar ƙorafe-ƙorafe da ƙin amincewa.
INEC ta buƙaci ’yan Najeriya da suka cancanta su yi amfani da damar da aka samu wajen yin rajista, sauya wurin zaɓe ko sabunta bayanansu, haka kuma ta nemi waɗanda suka yi rajista a zangon farko su ci gaba da tantance bayanansu tare da kai rahoton duk wani kuskure.

Sai dai hukumar ta ce har yanzu an dakatar da rajistar masu zaɓe a jihar Anambra da Abuja sakamakon ci gaba da harkokin zaɓe, inda ta ƙara da cewa za a sanar da sabbin ranakun sake farawa nan gaba.


