Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Syria: Mutane Sun Yi Zanga Zanga Domin Nuna Rashin Amincewa Da Korar Kurdawa A Birnin Aleppo Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas
Published: January 14, 2026 at 9:51 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Mutane shida sun rasa rayukansu yayin da wata babbar mota dauke da yashi ta kutsa cikin wani coci a yankin Epe na Jihar Lagos da yammacin Litinin.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:30 na dare a titin Hospital Road, lokacin da motar ke gangarowa zuwa zagaye (roundabout) sai birkinta ya lalace, direban ya rasa iko, motar ta kutsa cikin cocin.

Wasu masu ibada sun jikkata, yayin da jami’an agajin gaggawa na jihar Lagos suka isa wurin domin ceto wadanda suka makale.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa direban motar ya tsere bayan hatsarin.

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutane shida, tare da bayyana cewa motar ba ta da rajista.

An kai gawarwakin wadanda suka mutu dakin ajiye gawa, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: An Kaddamar Da Rijistar Zamani Ta Zamowa Mamba A Jam’iyar APC
Next Post: Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025.

Karin Labarai Masu Alaka

Ministan Kudin Najeriya: Bamu Samu Kudaden Da Muke Tsammani A Wannan Shekarar Ba Najeriya
Jihar Borno Ce Tayi Nasara A Gasan Karatun Al Qur’ani Na Kasa Najeriya
Ministan Tsaro Ya Umarci Janye Sojoji Daga Shingayen Bincike A Tituna Najeriya
Majalisar Tattalin Arzikin Najeriya Ta Bawa Gwamnan Kebbi Mukamin Kyautata Harkar Kiwo Najeriya
Shugaba Bola Tinubu Ya Tafi Turai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Gobara Ta Tashi A Hukumar FIRS Dake Abuja Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi
  • Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025.
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas
  • An Kaddamar Da Rijistar Zamani Ta Zamowa Mamba A Jam’iyar APC

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Rasha Ta Nuna Kudurin Cimma Zaman Lafiya Da Ukraine Amurka
  • Da Alamu Ronaldo Zai Buga Dukkan Wasanni Da Gasar Kofin Duniya A 2026 Wasanni
  • An Kai Hari Da Jirgi Mara Matuki A Kusa Da Matatar Mai Din Kasar Sundan Afrika
  • Gobara Ta Tashi A Hukumar FIRS Dake Abuja Najeriya
  • ‘Yan Sanda Sun Kama Masu Garkuwar da Mutane a Jihar Gombe Tsaro
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Litinin 11.17.2025 Rediyo
  • Kanal Sani: Idan ‘Yan-Ta’adda Zasu Mutunta Sulhu To Gwamnati Ta Duba Hakan Labarai
  • Kungiyar ECOWAS Ta Koka Game Da Yawan Juyin Mulki A Kasashen Afirka Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.