Gwamnatin Tarayyar Najeriya da ASUU sun kulla yarjejeniya ta farko a tarihi domin kawo karshen yawan yajin aiki a jami’o’in Najeriya
A wani muhimmin mataki da ake ganin zai sauya fasalin ilimin jami’a a Najeriya, Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) sun kulla wata babbar yarjejeniya da nufin inganta jin daɗin malamai, tabbatar da zaman lafiyar aiki da kuma kawo ƙarshen yawan yajin aikin da ya shafe shekaru yana durƙusar da jami’o’in ƙasar.
An bayyana yarjejeniyar ta shekarar 2025 tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU a ranar Laraba a Abuja, inda Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana ta a matsayin wani sabon shafi a tarihin ilimin gaba da sakandare a Najeriya.
A cewarsa, yarjejeniyar ba rubutun takarda bane kawai, illa alamar dawo da amana, girmamawa da kwarin gwiwa ga tsarin jami’o’in ƙasar bayan shekaru na rashin tabbas da yajin aiki.
Ministan ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa daukar mataki na musamman wajen fuskantar matsalar da ta dade tana addabar jami’o’i, tana lalata jadawalin karatu tare da rusa makomar dalibai miliyoyi.
“Wannan ne karon farko da Shugaban Ƙasa mai ci ya tsaya tsayin daka wajen fuskantar wannan ƙalubale kai tsaye, ya ba matsalar kulawar shugabancin da ta dace,” in ji Alausa, yana mai cewa gwamnatin ta zaɓi tattaunawa maimakon rikici, gyara maimakon jinkiri, da warware matsala maimakon surutu.
Daya daga cikin manyan abubuwan da yarjejeniyar ta ƙunsa shi ne ƙarin albashin malaman jami’a da kashi 40 cikin 100, wanda Hukumar Albashi, Kuɗaɗen Shiga da Albashi ta Ƙasa (NSIWC) ta amince da shi Sabon tsarin albashin zai fara aiki daga ranar 1 ga Janairu, 2026.
A karkashin sabon tsarin, albashin malaman zai haɗa da CONUASS da kuma ingantaccen alawus na kayan aikin koyarwa da bincike (CATA). An ƙarfafa CATA domin tallafa wa wallafa mujallu, halartar taruka, amfani da intanet, rajistar ƙungiyoyin ƙwararru da rubuce-rubucen littattafai, domin ƙara gogayya da rage guduwar ƙwararru zuwa ƙasashen waje.
Haka kuma, yarjejeniyar ta sake tsara alawus-alawus guda tara na Earned Academic Allowances, inda aka fayyace su sarai tare da danganta su kai tsaye da ayyukan da ake yi kamar kula da daliban digirin digirgir, aikin asibiti, jarrabawa da shugabancin harkokin ilimi.
A wani sabon salo da ba a taba gani ba a tsarin jami’o’in Najeriya, Gwamnatin Tarayya ta amince da wani alawus na musamman ga manyan malaman jami’a, wato Farfesoshi da Masu Karatu (Readers).
A karkashin wannan tsari, Farfesoshi za su rika karɓar naira miliyan 1.74 a shekara (naira 140,000 a wata), yayin da Readers za su karɓi naira 840,000 a shekara (naira 70,000 a wata).
Ministan ya ce an samar da wannan alawus ne domin ƙarfafa bincike, tsara takardu da inganta gudanarwa, ta yadda manyan malamai za su fi mayar da hankali kan koyarwa, renon matasa da kirkire-kirkire.
Ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatin Shugaba Tinubu za ta aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata a karkashin shirin Renewed Hope Agenda, tare da ci gaba da tattaunawa da gyare-gyare a fannin ilimi.
Masu ruwa da tsaki na ganin yarjejeniyar za ta kawo sabon zamani na kwanciyar hankali da inganci a jami’o’in Najeriya, tare da dawo da daidaito a jadawalin karatu da kuma sabunta fata ga dalibai da iyaye.
Ministan ya yabawa tawagogin tattaunawar bangarorin biyu, karkashin jagorancin Alhaji Yayale Ahmed daga bangaren Gwamnatin Tarayya da Farfesa Pius Piwuna daga ASUU, tare da tsohon shugabancin ASUU na Farfesa Emmanuel Osodeke, bisa rawar da suka taka wajen samar da wannan nasara.
A karshe, Alausa ya ce tarihi ba zai tuna wannan rana a matsayin ranar kaddamar da yarjejeniya kawai ba, illa ranar da Najeriya ta zabi tattaunawa, gaskiya da jajircewar shugabanci a matsayin hanyar warware matsalolin da suka dade suna addabar kasa.
Da yarjejeniyar ta kammala, al’ummar Najeriya na fatan cewa zamanin rufe jami’o’i na dogon lokaci zai zama tarihi, yayin da ake sa ran samun kwanciyar hankali, ƙwarewa da gogayya da jami’o’in duniya a fannin ilimi.


