A Laraban nan 19 ga watan Nuwambar 2025, ne hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka, wato Confederation of African Football (Caf) ta bayar da kyautar gwarzon ɗan ƙwallon kafa na nahiyar afirka ta shekarar 2025, inda Achraf Hakimi, dan wasan kasar Morocco ya lashe kyautar.
Bikin da ya gudana a jami’ar Mohammed VI Polytechnic University (UM6P) da ke Rabat, babban birnin Morocco. Ana bayar da wannan kyautar ne duk shekara ga daidaikun ‘yanwasa da sukayi kwazo, da kuma tawagogi domin jinjina musu kan bajintar da suka nuna a shekarar a fadin nahiyar Afirka.
Ana zaben gwarzon dan kwallo daga bangaren maza da mata, da masu horarwa, da kungiyoyi, dama sashin matasa. Ga jerin sunayen wadanda suka lashe kyautar CAF bana 2025:
Gwarzon dan wasan Afirka bangaren maza, Achraf Hakimi dan kasar Morocco mai buga wa ƙungiyar kwallon kafa ta Paris St Germain,
Muhammed Sala daga kasar Masar mai buga wa ƙungiyar kwallon kafa ta Liverpool, shine ya zamo na biyu, Victor Osimhen dan kasar Najeriya mai taka leda a ƙungiyar Galatasaray shine a mataki na uku.
Caf ta zabe Achraf Hakimi ne bisa taimakawa da yayi wa kungiyar sa ta PSG ta lashe kofin Champions League da babbar gasar Ligue 1 da Coupe de France har ma da Uefa Super Cup duk a cikin wannan shekarar.
Dan wasan ya kafa tarihi inda ya zamo dan wasa na farko a kasar Morocco tun bayan shekaru 27 da Mustapha Hadji ya lashe a 1998, haka kuma ya kasan ce mai tsaron baya na farko bayan shekaru 52 da ya lashe Kyautar, bayan Bwanga Tshimen dan wasan Kasar Zaire, da ya lashe a 1973.
A bangaren mata ma ‘yar wasan Afirka ta shekara: Ghizlane Chebbak daga kasar Morocco kuma ita ce mai tsaron raga ba kulub din Al-Hilal, ta Saudiya.
Ga wasu jerin sunayen wadanda suka samu Kyautar.
‘Yar wasan tsakiya ta shekara: Fiston Mayele
Mafi kyawon mai tsaron raga: Yassine Bounou
Mafi kyawon mai tsaron raga ta mace: Chiamaka Nndozie
Mafi kyawon matashin ɗan wasa: Othmane Maamma
Mafi kyawon matashiyar ‘yar wasa mata: Doha El Madani
Kocin Shekara: Bubista
Ƙungiyar shekara: Morocco U-20
Ƙungiyar shekara ta mata: Najeriya
Ƙungiyar shekara: Pyramids FC.
Mafi kyawon alkalin wasa na maza na CAF: Omar Artan
Mafi kyawon alkalin wasa ta mata a CAF: Shamirah Nabadda
Sai kuma Kyautar CAF hukumar ta karrama shugabannin kasashe uku saboda gudummawar da suka bayar ga ci gaban ƙwallon ƙafa a Afirka. Shugaban Kenya William Ruto, shugaban Tanzania Samia Suluhu Hassan.


