Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Iran Da Amurka Zasu Cimma Yarjejeniyar Nukiliya
Published: February 24, 2026 at 8:00 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Iran ko Farisa ranar talata ta bakin mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Majid Takht-Ravanci yace a shirye take ta dauki dukkan matakai domin ta cimma yarjejeniya da Amurka kan shirin Nukiliyarta, a dai dai lokacin da kasashen biyu suke shirye shiryen komawa teburin shawarwari.

Ana sa ran gudanar da shawarwarin ranar Alhamis a Geneva, kamar yadda wani babban jami’in Amurka ya fada ranar litinin, inda jakadun Amurka Steve Whitkoff da Jared Kushner, za su gana da tawagar wakilan Iran.

A farkon watan nan ne kasashen biyu suka koma kan teburin shawarwari, yayinda Amurka take jibge kayan yaki a yankin gabas ta tsakiya. Iran tayi barazanar zata kai hari kan sansanonin Amurka muddin aka kai mata hari.

Ahalinda ake ciki kuma, Ranar talata, wani jirgin yaki mai saukar ungulu na Iran, yayi hadari a kasuwan kayan gwari a yankin Isfahan na kasar, ya halaka matuka jirgin su biyu, da ‘yan kasuwa biyu.

Amurka, Labarai, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Somaliya Da MDD Sun Bayyana Cewa Kimanin Mutane Miliyan Shida Da Rabi Suna Fuskantar Barazanar Yunwa
Next Post: Tattaunawar Nukiliya Tsakanin Iran Da Amurka Yana Tasirin Akan Farashin Albarkatun Mai

Karin Labarai Masu Alaka

Mayakan Houthi Zasu Shiga Yakin Amurka Da Isra’ila Afrika
Amurka Zatayi Amfani Da Sansanonin Birtaniya Amurka
Majalisa A Kasar Somaliya Ta Amince Da Sauya Tsarin Mulkin Kasar Afrika
Rasha: Zamu Ba Gwamnatin Venezuel Gudunmawa Sauran Duniya
‘Yan Bindiga A Mali Sun Kashe Direbobin Manyan Motoci Afrika
Kasar Ukraine Ta Yabawa Tarayyar Turai Bisa Bata Tallafi Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa Afrika
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • Guinea Bissau Ta Tsaida Gwaje-Gwajen Allurar Rigakafin Shawara A Kasar Labarai
  • An Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman Don Neman Zaman Lafiya Labarai
  • Matatar Man Dangote Zata Bada Kwangilar Sayar Da Gas Da Man Jirage Afrika
  • Dakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Yan Kungiyar Lakurawa Afrika
  • Hukumar Hisbah Ta Kona Barasar Dubban Nairori A Katsina Labarai
  • Rasha Takai Mummunan Hari Birnin Kyiv Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.