Shugaban Najeriya ya bada sanarwar cewa an kwato dukkan ‘yan mata 24 da aka sace daga wata makarantar sakandaren mata ta gwamnati dake Jihar Kebbi a Arewa maso yammacin kasar.
An sace wadannan dalibai mata ne a ran 17 ga watan Nuwamba, inda a lokacin ‘yan sanda suka ce su 25 aka sace.
Wata sanarwar da aka bayar yau Talata ta ambaci shugaba Bola Ahmed Tinubu yana fadin cewa an kwato dukkan dalibai 24 da aka sace. Ba a yi karin haske kan yadda aka kwato su ba.
Shugaba Tinubu yace yayi farin cikin cewa an samo wadannan ‘yan mata 24, yana mai cewa tilas ne a yanzu a dauki matakan tabbatar da cewa irin wannan abu bai sake faruwa ba a wuraren da suke fuskantar matsalolin tsaro ba.
Wannan hari na Kebbi na daga cikin hare-haren sace mutane masu yawa da aka yi cikin ‘yan kwanakin nan a Najeriya.


