Ƙungiyar Kwallon Kafa ta Barcelona ta lashe Kofin Spanish Super Cup 2025.
Dan wasan Barcelona Raphinha ya zura kwallaye biyu yayin da Barcelona ta lashe gasar Spanish Super Cup bayan ta yi nasara a kan babbar abokiyar Hamayyarta Real Madrid da ci 3-2 a wasan karshe ranar Lahadi a Jeddah.
Wasan da aka buga a filin wasa na King Abdullah Sports City ya zama abin birgewa, inda aka zura kwallaye hudu a karshen farkon lokacin.

Yayin fara wasan dai, Barcelona ta tabbatar da mamaye iko a wasan kafin a tafi hutun rabin lokaci a minti na 36 Raphinha ya jefa kwallo ta farko a ragar Real Madrid.

Real ta rama kwallo a karin mintuna biyu na farkon ta kafar Vinicius Jr.
Barcelona ta zura kwallon ta na biyu a karin mintuna 4 na kafin tafiya hutun rabin lokaci ta kafar Robert Lewandowski kuma ya samu rauni aka canje shi a wasan.
Daga bangaren Real Madrid, dan wasan ta Gonzalo Garcia ya yi nasarar zura kwallo a raga, inda kwallon ta buga sandar kafin ta ketare layin, wanda hakan ya sake bai wa ƙungiyoyin damar yin daidai kafin lokacin da ƙungiyoyin suka tafi hutun rabin lokaci.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Raphinha ya sake jefa kwallo a minti na 73 a ragar Real, ƙwallon da ya buga ta yi baudiya wa mai tsaron raga na Real, Thibaut Courtois bayan ta taba ƙafar dan wasan Real, ta shiga raga.
Yayin da agogo ya yi ƙasa da mintuna 90, wasa tayi zafi inda aka rage wa Barcelona dan Wasa daya suka rage ‘yan wasa 10 bayan da aka bada Jan kati WA Frenkie de Jong saboda ketar da ya yi wa Kylian Mbappe.
Haka dai aka tashi a wasan Barcelona ta samu nasarar lashe Kofin Spanish Super Cup na bana.
Ana shirya ga sanne duk shekara bayan kammala karka wasa inda ake zaben kungiyoyin kwallon kafa hudu da suka fi kwazo daga gasannen kasar Spain.
Ƙungiyoyin da suka halarta wannan shekara sune Barcelona, Real Madrid, Atletico Madrid da kuma Bilbao.


