Mayakan Boko Haram sun sace sabon mataimakin shugaban karamar hukuma da kansiloli a jihar Borno dake arewacin Najeriya
Wasu da ake zargin mambobin kungiyar Boko Haram ne sun sace sabon Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Biu da wasu kansiloli biyu, a kan hanyar Kamuya Buni Yadi, a Jihar Borno.
Majiyoyi da ke kusa da iyalansu sun bayyana sunan Mataimakin Shugaban a matsayin Alhaji Saidu. Kansilolin biyu masu wakiltar mazabun Zarawuyaku da Miringa.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa an zaɓi wadanda aka sace ne kwanaki biyar da suka gabata, a zaben kananan hukumomi da aka gudanar ranar Asabar da ta wuce.
Daya daga cikin majiyoyin ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Laraba, kuma ya shafi wasu matafiya da ke cikin wata motar Hizbah Hummer.
“Gaskiya ne, Alhaji Saidu da kansilolin biyu an sace su ne da hannun wadanda ake zargin ‘yan Boko Haram/ISWAP ne, a tsakanin kauyen Kamuya da hanyar Buni Yadi.
“An sace su tare da wasu fasinjoji da ba a tantance su ba, wadanda ke tafiya cikin wata motar Hizbah daga garin Potiskum na Jihar Yobe zuwa Biu.
“Daya daga cikin kansilolin da aka sace shi ne tsohon Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Biu na nan kusa kuma muna rokon gwamnati da hukumomin tsaro su kara kaimi wajen ceto su da sauran wadanda aka kama” in ji shi.
Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, bai yi nasara ba, domin ba a samu damar tuntubarsa ta waya ba, haka kuma bai amsa sakonnin da aka aike masa ba.


