Gwamna Inuwa Yahaya zai aiwatar da sabon tsarin bunƙasa Rigakafin cutar Polio a yan kunan Karkara tare da haɗin gwiwa da gidauniyar Gates.
A ranar Alhamis ne Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya karɓi baƙoncin wata tawaga daga Gidauniyar Gates, ƙarƙashin jagorancin Daraktar yaki da Cutar Polio ta duniya, Kathy Neuzil.
Taron wanda aka gudanar a masauƙin Gwamnan na Gombe dake Abuja, ya ta’allaƙa ne kan zurfafa haɗin gwiwa don inganta rigakafin cutar shan inna, musamman a yankunan dake fama da matsalar tsaro a Arewacin kasar.
Tattaunawar ta kuma lalubo matakan inganta tsaro, da haɗa kan al’umma da tsare tsaren sanya ido, tare da fayyace lokaci da matakan ƙara ƙaimi wajen ganin an kawar da Cutar shan Inna daga Najeriya.
A matsayinsa na Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa kuma shugaban Kwamitin Majalisar Tattalin Arzikin kasa kan kawar da cutar shan inna, Gwamna Inuwa Yahaya ya jaddada ƙudurinsa na tallafawa ƙoƙarin da al’umma ke yi na kawar da cutar.
Ya yaba da muhimmiyar rawar da Gidauniyar Gates ta taka tare da jaddada buƙatar ci gaba da yin haɗin gwiwa, musamman a wuraren da rashin tsaro ke haifar da ƙalubale ga ayyukan rigakafi.
“Gaskiya ne cewa wasu jihohi suna fama da manyan ƙalubalen tsaro dake hana ma’aikatan rigakafi kaiwa ga wasu yankuna, amma a matsayina na shugaban kwamitin majalisar tattalin arziƙin kasa kan kawar da cutar shan inna, zan ci gaba da jan hankalin takwarorina da hukumomin tsaro dama wadanda abin ya shafa don ƙarfafa hanyoyin kaiwa ga irin waɗannan yankuna kuma idan akwai buƙatar matakan tsaro na musamman don kare ma’aikatan rigakafin, mun shirya tsaf don samar da hakan.”
Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa tuni aka fara ɓullo da sabbin dabarun tsaro tare da bayyana ƙwarin gwiwar cewa waɗannan matakai za su inganta hanyoyin samun sauƙi da kuma tabbatar da tsaron lafiyar ma’aikatan dake sahun gaba a gangamin rigakafi.
Ya kuma baiwa gidauniyar tabbacin ci gaba da bada goyon bayansa wajen samar da haɗin kai a tsakanin gwamnonin Arewa don kyautata harkar rigakafi da kuma ɗorewar gangamin kawar da cutar.
Ya buga misali da “tsarin Gombe”, wanda aka gina bisa ƙwaƙƙwaran tsarin damawa da al’umma, tsarin da aka shimfiɗa bisa ingantacciyar manufa, a matsayin tsarin da za a iya ɗabbaƙawa a faɗin yankin don samun sakamako mai kyau.
A nata jawabin, Daraktar Gidauniyar ta GF Global Polio, Kathy Neuzil, ta bayyana damuwa kan yadda al’ummomi da dama ke fama da matsalar tsaro, ta kuma nemi haɗin kai da Gwamna Inuwa Yahaya, a matsayinsa na shugaban ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa kuma shugaban kwamitin yaƙi da cutar shan inna na Majalisar Tattalin Arziƙin Ƙasa NEC, don haɗa kai da shugabanni a jihohi da hukumomin tsaro wajen samar da kariya ga ma’aikatan lafiyan dake gudanar da rigakafin cutar ta Polio.
Ta yabawa jagorancin Gwamnan da irin gagarumin ci gaban da aka samu a jihar Gombe, inda ta bayyana cewa masu bada tallafi suna sanya ido sosai saboda ganin jajircewar shugabanni, da yadda ake damawa da al’umma da kuma nasarorin da ake samu.
“Mun yaba da gagarumin ƙuduri da jajircewar da muka gani a Jihar Gombe,” in ji Neuzil.
Ta ƙara da cewa, “Yin aiki tare da gwamnatocin jihohi, musamman a ƙarƙashin jagorancinka a Kungiyar Gwamnonin jihohin Arewa, yana ba mu ƙwarin gwiwar cewa za a iya cike giɓin da ake da shi.”
Gwamna Inuwa Yahaya ya samu rakiyar kwamishinan lafiya na jihar Gombe, Dr. Habu Ɗahiru da Sakataren Hukumar Taimakekeniyar Lafiya ta GoHealth, Dr. Abubakar Musa Yahaya da Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta jihar Gombe, Dr. Abdulrahman Shuaibu Jimeta.
Tawagar Gidauniyar ta Gates ta haɗa da Daraktar kawar da Cutar Polio ta Duniya Kathy Neuzil da Mataimakan Darakta Yusuf Yusufari da Andrew Stein.


