A gumurzun yau Lahadi 14 ga watan Disamba da aka fafata a jihar Nasarawa, tsakanin: Manu daga ɓangaren Guramada da kuma Sola daga Jamus, sai kuma Autan Auta daga ɓangaren Jamus sai kuma Bagobirin Guramada da Kuma Ayi Kullum da Dan Alin Bata isarka.
Dukkanin wasannin sun gudana,in banda na Ayi Kullum wanda aka sauya ma shi abokin karawa da Dan Alin Bata Isarka sabida rashin Halartar Dogon Doga a wasan.
Wasannin duka an buga ba tare da wani ya yi nasara akan dan uwansa ba, a ɗaukacin turamen uku na kowace fafatawar.
A jihar Sokoto kuwa, wasanni ya gudana ne kamar haka:
Shagon Nadada na Kudu yayi nasar halaka Garkuwan Kurma na ɓangaren Guramada Autan sani, na ɓangaren Jamus sun gwabza da shagon Hussaini Ka’oje na ɓangaren Guramada, inda Shagon Hussaini ya sha da ƙyar.
Bahagon Ramdan da shagon jango su ja zare, inda suka nunawa juna yasta, amman aka maida wasan zuwa ranar Litinin.


