Gwamnatin Najeriya ta samu nasarar ceto yara 100 da aka sace a Makarantar St. Mary’s a jihar Neja.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, gwamnatin tarayya ta samu nasarar kubutar da yara 100 da aka sace daga Makarantar St. Mary’s Private Catholic Primary da Secondary School, da ke Papiri cikin ƙaramar hukumar Agwara, Jihar Neja.
Yaran, waɗanda aka sace a wani harin da masu garkuwa da mutane suka kai, yanzu haka dai suna cikin koshin lafiya, kamar yadda majiyoyi suka bayyana.An ce gwamnati ta yi aiki tare da jami’an tsaro da hukumomin jihar domin ganin an dawo da yaran cikin aminci.


