Hukumar Tsaron Civil Defence Ta Tura Jami’ai 786 Don Tabbatar da Tsaro a Gombe Ranar Kirsimeti da Sabuwar Shekara

Rundunar Tsaro ta Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) reshen jihar Gombe, ta bayyana tura jami’anta 786 domin tabbatar da tsaro a yayin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara a fadin jihar.
Kwamandan NSCDC na jihar Gombe, Muhammad Bello, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce rundunar ta kammala dukkan shirin da ya dace don tabbatar da zaman lafiya a lokacin bukukuwan karshen shekara.
Ya ce jami’an da aka tura sun hada da sashen leken asiri, kwararrun masu magance tashin bama-bamai, da kuma rundunar sintiri ta musamman da ke aiki da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da cewa an gudanar da bukukuwan cikin kwanciyar hankali.
Kwamandan ya yi kira ga al’umma da su bawa jami’an tsaro hadin kai, tare da bayar da bayanai cikin gaggawa idan suka ga wani abu da ke haifar da barazana ga zaman lafiya.
Ya kuma gargadi masu shirin tayar da hankali da cewa za su fuskanci hukunci mai tsanani idan aka kama su da aikata laifi a wannan lokaci.
Rundunar NSCDC ta bukaci jama’a da su yi bukukuwa cikin lumana tare da kiyaye dokokin kasa.


