Kamfanin hakar ma’adinai na kasar Canada mai suna Barrick, a hukumance ya fara ci gaba da aikin hakar ma’adinai, kamar yadda wata kasida daga kamfanin, da kamfanin dillancin labarai ta Reuters ya bayyana.
Kamar yadda bayani da daraktan ayyuka na kamfanin mai kula da shiyyar Afirka da gabas da ta tsakiya Sebastian Bock ya aika, kamfanin na Barrick zai fara aiki sannu a hankali, inda zai fi maida hankali wajen horas da ma’aikata da ‘yan kwangila.
Sassan biyu sun cimma yarjejeniya cikin watan jiya cewa zasu warware duk wata takaddama tsakanin sassan biyu, bayan shawarwari da suka yi a tsawon shekaru biyu. kuma zasuyi aiki da wani sabon kuduri da gwamnatin soja a kasar ta bullo dashi ya tilastawa kamfanin Barrick dakatar da aikinsa.
A halin yanzu dai Barrick ya amince zai biya gwamnatin Mali dala milyan 430, kum, amakon jiya ne wani alkali ya umarci gwamnati ta mayarwa amfanin Barrick zinari ton 3 da aka kiyasta akan kudi dala milyan dari hudu wannan mataki yasa farashin hanun jarin kamfanonin Barrick ya tashi da kamar kashi daya a kasuwar saye da sayar da hannayen jari a Canada.
Sannan kuma, babban wurin hakar ma’adnai na kasar Guinea da ake kira Simandou, da gwamnatin mulkin sojan kasar take ji da shi ya fara sallamar dubban ma’aikata, a dai dai lokacinda ya fara jigilar ma’adinan karafa zuwa ketare.


