Dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) sun ƙara zafafa hare-haren su kan mayakan Boko Haram da ISWAP a jihar Borno, wanda ya haifar da gagarumar nasara a yaki da ta’addanci.
A cewar sanarwar da jami’in hulɗa da manema labarai na Rundunar Haɗin Gwiwa a Arewa Maso Gabas, Laftanal Kanar Sani Uba ya fitar, dakarun sun tilasta wa ‘yan ta’adda 11 su miƙa wuƙa a yankin Azir–Wajiroko tare da mayar da AK-47 da harsasai daban-daban.
A ranar 9 ga Janairu, 2026, dakarun sun gudanar da gagarumin farmaki a yankin Bula-galda, inda suka lalata sansanonin ‘yan ta’adda a Dagumba, Bonne, Yaganari, Gosuri da Umchile, kuma lokacin farmakin, an rusa mafaka da dama, an katse hanyoyin samar musu da kayan aiki, kuma an kwato tutocin ta’addanci, bindigogi da makamai.
A wasu farmakin da suka gudana a yankunan Yale da Bula Gaida, sojojin sun sake rusa cibiyoyin kayan aiki na ‘yan ta’adda, tare da kwato bindigogi, harsasai da bindigar gurneti.
Haka kuma, bisa sahihan bayanan leƙen asiri, dakarun sun fafata da mayaƙan JAS/ISWAP a tsakanin kauyukan Sojiri da Kayamla, inda suka kashe ‘yan ta’adda 8.
An kuma kama wasu mutane biyu da ake zargin suna ba da kayan aiki ga ‘yan ta’adda a ƙaramar hukumar Gubio.
Rundunar Sojojin Najeriya ta jaddada kudirinta na dawo da zaman lafiya a Arewa maso Gabas tare da roƙon al’umma da su ci gaba da ba da sahihan bayanai don taimaka musu a yaki da ta’addanci.


