Shugaban Nigeria, Bola Tinubu, ya turawa majalisar dattijai sunayen mutane biyu da zasu shugabanci sashen lura da alabarkatun man fetur na kasar, don tantancewa, bayan da shugabbannin baya suka yi murabus, biyo bayan dambarwar da aka tafka tsakanin wani sashe da attajri Alhaji Aliko Dangote.
Tinubu ya fidda sabbin mutanen ne bayan da Gbenga Komolafe, da Farouk Ahmed masu kula da sassa daban na alabarkatu man fetur na kasa suka ajiye aikin su.
Dangote ya zargi Farouk Ahmed da barin ana shigo da kayyayakin man fetur da aka yanke musu farashi, wanda ke kawo barazana ga matatun mai na kasa, ciki har da matatar man sa ta Lagos da ake samun gangar mai 650,000 a kowacce rana, Wadda ita ce mafi girma a Afirka.
Ranar Laraba Dangote ya mika takardar tuhuma kan Farouk Ahmed ga daya daga cikin hukumomin da ke yaki da wadaka da tattalin arzikin kasa (ICPC).
A nasa bangaren kuma, Gbenga Komolafe, wanda ya fara gwanjon filayen man fetur a kwanan nan ya haura da Dangote, saboda gazawar sa wajen dabbaka dokar da zata bukaci kamfanonin mai su fifita matatun cikin gida.


