Ranar lahadi shugaba Donald Trump na Amurka yace babu man fetur ko sisin kwabo na Venezuela da zai sake zuwa Cuba, yana mai cewa ya kamata shugabannin kwaminis na kasar su nemi kulla yarjejeniya da Amurka kafin lokaci ya kure.

Kasar Cuba tana samun mafi yawan man fetur dinta daga Venezuela, amma babu jirgin mai ko guda daya da ya tashi zuwa Cuba daga can tun bayan da sojojin Amurka suka damko shugaba Nicolas Maduro.
Shugaba Miguel Diaz-Canel na Cuba yayi watsi da barazanar da shugaba Trump yayi a kafofin sada zumunci, yana mai cewa ai Amurka ba ta da hurumin sanya Cuba ta kulla wata yarjejeniya.
Diaz-Canel ya fada a shafin X cewa Cuba, kasa ce ‘yantacciya, mai cin gashin kai, kuma babu wani mahalukin da zai fada mata ga abinda zata yi.
Yace Cuba ba ta kai hari, amma Amurka ta yi shekaru 66 tana kai mata farmaki, yana mai fadin cewa a shirye suke su ci gaba da kare kasarsu.


