Shekara ta 2025 na da muhimmanci ga Najeriya ta fuskar siyasa, tattalin arziki da tsaro don ita ce shekara ta 3 ta wa’adin mulkin shugaba Tinubu gabanin zaben 2027.
An wayi gari a watan Maris shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta baci a jihar Ribas da hakan ya dakatar da gwamna Siminalayi Fubara na tsawon wata 6 biyo bayan turka-turkar madafun ikon jam’iyya ko tasirin mulki tsakanin gwamnan da wanda ya gada tsohon gwamna ministan Abuja Nyesom Wike.
Duk da masu sharhi na ganin hakan na cike da muradun siyasa da biyewa Wike don rawar da ya taka ta kange dan takarar adawa Atiku Abubakar daga lashe zabe a 2023, shugaba Tinubu ya dage dokar kuma hakan ya dawo da Fubara karaga.
A dabarun siyasa Fubara ya sauya sheka ya dawo jam’iyyar APC ta shugaba Tinubu inda ya ba da hujja da nuna guguwar nan in ba da taimakon shugaba Tinubu ba da wani labarin a ke yi.
Bayan jita-jitar yunkurin juyin mulki da hukumomi ba su tabbatar da rundunar sojan Najeriya ta ba da bayanin tsare hafsoshi 16 da nuna sun aikata wasu laifuka ne da su ka sabawa aiki. Daga bisani shugaba Tinubu ya yi garambawul ga hafsoshin soja ya sauke su in ban da babban hafsan bayanan sirri. Har ila yau shugaba Tinubu ya nada tsohon babban hafsan rundunar soja Janar Christopher Musa a matsayin ministan tsaro bayan murabus din babban minista Muhammad Badaru. Masana tsaro irin su Dokta Yahuza Getso sun yi sharhi.
Duk da yunkurin Najeriya da sauran kasashen ECOWAS na dawo da kasashe uku da su ka fada mulkin soja, Nijar, Burkinafaso da Mali, ya ci tura har zuwa watan Yuli. Ministan wajen Najeriya Yusuf Tugga ya ce sun yi duk abun da ya dace don dawo da kasashen masu taken AES
Yayin da shugaba Tinubu ya nada Injiniya Saidu Muhammad ya maye gurbin shugaban hukumar raba fetur a cikin kasa Injiniya Farouk Ahmed wanda ya yi murabus bayan takaddama da attajiri Aliko Dangote bisa zargin amfani da kudi fiye da samunsa, majalisar dokoki kuma ta amincewa shugaban amfani da kasafin kudin bara da na bana har zuwa watan Maris na badi. Wannan dai shi ne karo na farko da hakan ke faruwa. Dan majalisar Abubakar Hassan Fulata ya yi bayanin kariya kan matakin da ‘yan majalisa su kea mince.
Hakanan shugaba Tinubu ya ba da umurnin janye jami’an ‘yan sanda daga tawagar rakiyar manyan mutane don tura su inda za su kula da asalin aikinsu na samarwa al’umma tsaro.
Ita kuma babbar jam’iyyar adawa ta PDP na kara rage tasiri don gwamnonin jam’iyyar na ficewa zuwa APC inda shugaban da jam’iyyar ta zaba a babban taron Badun Barista Tanimu Turaki ke fama da kalubale daga bangaren jam’iyyar na magoya bayan Wike.
Dambarwar iko da babban ofishin jam’iyyar, ya sa Turaki zargin gwamnatin APC da makarkashiya, in da ya bukaci shugaba Trump ya kawo dauki.
Jigon jam’iyyar tsohon gwamnan Jigawa Sule Lamido da ya kai jam’iyyar kara kotu don hana shi tsayawa takarar shugabanci, ya nuna alamun zai iya barin jam’iyyar don ya ce in ba ta gyara ba za ta iya rasa dukkan mukamai a zaben gaba.
Ba mamaki kai korafin Bishop Wilfred daga Binuwai zuwa majalisar dokokin Amurka kan zargin yi wa mabiya addinin kirista kisan kare dangi a Najeriya, ya ja wani harin Amurka a yankin jihar Sokoto da har yanzu ba cikekken bayanin yanda lamarin ya kasance, duk da gwamnatin Najeriya ta ce ta na da masaniya.
Cikin manyan juyayi a shekarar ta 2025 akwai rasuwar tsohon shugaba Buhari bayan kwanciya a asbiti a London, sai kuma Shehun malamin Sunnah Dokta Idris Abdul’aziz Dutesn Tanshi wanda ya rasu a gidansa a Bauchi bayan fama da jinya.
Allah ya yi wa babban Shehun malamin Islama na darikar Tijjaniya Sheikh Dahiru Usman Bauchi rasuwa, shi ma a Bauchi inda Sheikh Sharif Ibrahim Sale ya jagoranci yi ma sa sallar jana’iza.
Fatan alheri ga dukkan masu sauraro a yayin da mu ke marabtar sabuwar shekarar 2026.


