Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Syria: Mutane Sun Yi Zanga Zanga Domin Nuna Rashin Amincewa Da Korar Kurdawa A Birnin Aleppo Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Wasu Zakaru Da Suka Samu Karramawar Hukumar CAF Ta Afrika
Published: November 20, 2025 at 2:29 PM | By: Yusuf Aliyu Harande

A Laraban nan 19 ga watan Nuwambar 2025, ne hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka, wato Confederation of African Football (Caf) ta bayar da kyautar gwarzon ɗan ƙwallon kafa na nahiyar afirka ta shekarar 2025, inda Achraf Hakimi, dan wasan kasar Morocco ya lashe kyautar.

Bikin da ya gudana a jami’ar Mohammed VI Polytechnic University (UM6P) da ke Rabat, babban birnin Morocco. Ana bayar da wannan kyautar ne duk shekara ga daidaikun ‘yanwasa da sukayi kwazo, da kuma tawagogi domin jinjina musu kan bajintar da suka nuna a shekarar a fadin nahiyar Afirka.

Ana zaben gwarzon dan kwallo daga bangaren maza da mata, da masu horarwa, da kungiyoyi, dama sashin matasa. Ga jerin sunayen wadanda suka lashe kyautar CAF bana 2025:

Gwarzon dan wasan Afirka bangaren maza, Achraf Hakimi dan kasar Morocco mai buga wa ƙungiyar kwallon kafa ta Paris St Germain,

Muhammed Sala daga kasar Masar mai buga wa ƙungiyar kwallon kafa ta Liverpool, shine ya zamo na biyu, Victor Osimhen dan kasar Najeriya mai taka leda a ƙungiyar Galatasaray shine a mataki na uku.

Caf ta zabe Achraf Hakimi ne bisa taimakawa da yayi wa kungiyar sa ta PSG ta lashe kofin Champions League da babbar gasar Ligue 1 da Coupe de France har ma da Uefa Super Cup duk a cikin wannan shekarar.

Dan wasan ya kafa tarihi inda ya zamo dan wasa na farko a kasar Morocco tun bayan shekaru 27 da Mustapha Hadji ya lashe a 1998, haka kuma ya kasan ce mai tsaron baya na farko bayan shekaru 52 da ya lashe Kyautar, bayan Bwanga Tshimen dan wasan Kasar Zaire, da ya lashe a 1973.

A bangaren mata ma ‘yar wasan Afirka ta shekara: Ghizlane Chebbak daga kasar Morocco kuma ita ce mai tsaron raga ba kulub din Al-Hilal, ta Saudiya.

Ga wasu jerin sunayen wadanda suka samu Kyautar.

‘Yar wasan tsakiya ta shekara: Fiston Mayele

Mafi kyawon mai tsaron raga: Yassine Bounou

Mafi kyawon mai tsaron raga ta mace: Chiamaka Nndozie

Mafi kyawon matashin ɗan wasa: Othmane Maamma

Mafi kyawon matashiyar ‘yar wasa mata: Doha El Madani

Kocin Shekara: Bubista

Ƙungiyar shekara: Morocco U-20

Ƙungiyar shekara ta mata: Najeriya

Ƙungiyar shekara: Pyramids FC.

Mafi kyawon alkalin wasa na maza na CAF: Omar Artan

Mafi kyawon alkalin wasa ta mata a CAF: Shamirah Nabadda

Sai kuma Kyautar CAF hukumar ta karrama shugabannin kasashe uku saboda gudummawar da suka bayar ga ci gaban ƙwallon ƙafa a Afirka. Shugaban Kenya William Ruto, shugaban Tanzania Samia Suluhu Hassan.

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2025/11/RAHOTON-WASANNI-SAFE-20-11-2025.mp3
Wasanni

Post navigation

Previous Post: Shirin Dare 2030 UTC Yau Laraba 11.19.2025
Next Post: Trump Da Bin Salman Da Wasu Kasashe Za Su Sa Hannu A Rikicin Sudan

Karin Labarai Masu Alaka

‘Yan Wasan Kwallon Kafar Najeriya A Shirye Suke Wasanni
Magoya Bayan Nice Sun Kai Hari Wa ‘Yan Wasansu Wasanni
Kocin Ranchers Bees Ya Yi Murabus Wasanni
Wikki Tourist FC: Ta Sallami ‘Yan Wasa Hudu Wasanni
CAF, Zata Ci Tarar Wasu Kasashe AFCON 2025 Wasanni
Liverpool Tayi Rashin Nasara A Wasanni Tara Wasanni

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi
  • Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025.
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas
  • An Kaddamar Da Rijistar Zamani Ta Zamowa Mamba A Jam’iyar APC

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Gwamnan Neja Bago Na Cin Zarafin Talakawan Da Suka Zabe Shi Labarai
  • Wikki Tourist FC: Ta Sallami ‘Yan Wasa Hudu Wasanni
  • Tsohon Alkalin Alkalai A Najeriya Ya Rasu Yana Da Shekaru 71 Labarai
  • Shugaba Bola Tinubu Ya Tafi Turai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kasar Ukraine Ta Yabawa Tarayyar Turai Bisa Bata Tallafi Labarai
  • Kamfanin Hakar Ma’adanai Na Kasar Kanada Ya Cigaban Da Aikinsa Labarai
  • ‘Yan Tawayen Kungiyar M23 Sun Tsagaita Sakamakon Rokon Da Amurka Tayi Amurka
  • Anfara Tantance Lafiyar Maniyyatan Jihar Gombe Kiwon Lafiya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.