Rahotanni daga Jihar Nejan Najeriya na nuna cewa wata mace daga cikin mutane 17 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su ta tutu a hannun ‘yanfashin dajin.
Tun a ranar 1/8/2025 ‘yanbindigar suka kutsa garin Ibeto a karamar Hukumar Magama suka kwashe mutane goma sha bakwai 14 daga cikin su matane sai kuma maza uku.
Masu garkuwar bukaci kudin fansa na naira milyan 150 kafin su sako wadan nan mutane, kuma har ya zuwa wannan lokaci mutanen garin na Ibeto basu hada wadannan kudaden ba.
Muhammad Kabir mazaunin garin na Ibeto yace tabbas sun samu labarin mutuwar daya daga cikin matan, sannan kuma wata matar guda da aka wuce da ita da ciki ta haihu a ranar Laraban nan da ta gabata.
Har yau dai babu wani bayani mai karfi daga bangaren gwamnatin Jihar Nejan akan kokarin karbo wadannan mutane na garin Ibeto,
Sai dai Shugaban karamar Hukumar ta Magama Dr. Muhmud Muhammad yace matsalar tana damunsu kuma cikin ikon Allah zasu samu mafita.
Kwamishinan Ma’aikatar kula da manyan Makarantun Jihar Nejan Farfesa Yakubu Auna, yace amatsayin su na masu ruwa da tsaki a yankin suna kokarin ganin an samu nasarar karbo wadannan mutane.
Mutuwar wannan baiwa Allah ta Ibeto a hannun ‘yanbindigar dai yana wuwa ne a dai dai lokacin da Kwamishina a hukumar Zabe ta jihar Neja Barista Ahmed Muhammad Borgu da Kuma tsohon shugaban Hukumar bada Ilimi bai daya ta jihar Nejan Hon. Alhasan Bawa Niworu suka share kimanin watanni uku a hannun ‘yanfashin da a yanzu haka bayanai ke nuna masu garkuwar sun bukaci milyan 300 kafin su sako su.
A yanzu dai hukumomin Jihar Nejan sun maida hankali wajan kokarin kubutar da sauran yara kimanin 200 da akayi garkuwa dasu a makarantar St Mary mallakar Cocin Katolica dake garin Papiri duk a Jihar Nejan.

