‘Yan bindiga sun kashe mutane kimanin 100 a wasu hare-haren da suka kai kan wasu kauyuka biyu a yankunan tsakiya da kuma arewacin Najeriya, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da neman mutanen da suka kubuta da rayuka suke kuma farautar ‘yan bindigar.
A jihar Kwara dake yankin tsakiyar Najeriya, ‘yan bindiga sun kai farmaki a wani kauye mai suna Woro, inda suka kashe mutane masu yawa.
Gwamnan jihar ta Kwara, Abdulrazaq Abdulrahman, wanda ya ziyarci inda abin ya faru ranar laraba tare da wasu kwamandojin soja da sojoji kimanin dubu 1, ya fadawa wani dan jarida dake zaune a Amurka, Farooq Kperogi, cewar sun tabbatar da mutuwar mutane 75 ya zuwa lokacin da suka yi magana, amma kuma adadin yana iya karuwa yayin da ake ci gaba da neman mutanen da suka bace.
Tun da farko, wani dan majalisa mai wakiltar yankin ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa mutane har 170 suka mutu.
Shi ma kwamandan birged ta 22 ta dakarun Najeriya dake Ilorin, Birgediya Janar Nicholas Rume, ya fadawa Malam Farooq Kperogi cewa sun shawo kan lamarin a yanzu.
Wannan shine hari mafi muni da aka gani cikin shekarar nan a wannan yanki mai iyaka da jihar Neja, inda ake fama da hare-haren ‘yan bindiga masu kai farmaki a kan kauyuka da satar jama’a don yin garkuwa da su tare da satar dabbobi.
Dan majalisar da yayi magana da kamfanin dillancin labaran Reuters ta waya, Saidu Baba Ahmed, yace ‘yan bindigar sun tattara mutanen garin, suka daddaure hannayensu ta baya, sannan suka kashe su. Haka kuma ‘yan bindigar sun cinna wuta a gidaje da shaguna.
A wani harin na daban kuma, ‘yan bindiga sun kashe mutane akalla 21 a jihar Katsina dake arewacin Najeriya, inda ‘yan sanda da mazauna garin suka ce wadannan mahara sun bi gida-gida suna harbe mutane.
Wannan harin ya kawo karshen sulhun da aka yi a tsakanin mutanen wannan gari da ‘yan bindigar watanni 6 da suka shige.
Wannan hari na jihar Katsina ya nuna irin halin kaka-ni-ka-yin da mutane suke ciki a yankunan karkara na arewacin Najeriya, wadanda suka nemi yin sulhu da ‘yan bindigar da suke addabar su.
Mazauna irin wadannan kauyuka a akasarin lokuta suna harhada kudade da abinci domin bawa wadannan ‘yan bindiga da nufin neman su kyale su.


