
Rayuwar duk wani taliki na kan ka’idar karewa wata rana kuma hakan ne ya yi ta faruwa tun tsawon tarihin halitta. Mutum na farko wato Annabi Adamu alaihis salam ya bar duniyar nan. Duk wani mai daraja zai bar duniya. Mu tuna mafi darajar halitta Annabi Muhammadu mai tsira da aminci shi ma ya yi wafaati. In haka ne ai kowa ma na da iya shekarun da zai yi a doron kasa sannan ya dandani mutuwa! Marigayi mai waka Alhaji Adamu Danmaraya Jos na cewa “mutuwa rigar kowa..da da hali da ya tube..amma babu hali” kuma hakan ya tabbata don Danmaraya ya rasu shekarun baya. Mutuwa tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta zo ba tare da tsammanin hakan ba. Wannan kuwa don dama an saba sanin ko jin yanda marigayin kan tafi London don neman magani musamman daga lokacin day a hau kujerar shugabancin Najeriya tsakanin shekara ta 2015-2023. Akwai wata doguwar jinya da marigayin ya yi inda ya zauna a asibiti a London wajen wata 3 amma Allah cikin ikon sa ya dawo ya cigaba da mulkin sa. A wancan lokacin jama’ar kasa sun yi ta yi ma sa addu’ar Allah ya ba shi lafiya kuma Allah ya amsa addu’ar ya ba shi sauki ya dawo Abuja. Kasa ta dau murna bisa amsa addu’ar da Allah madaukakin sarki ya yi wajen ba wa wannan bawan na sa da ‘yan kasa ke kyautatawa zaton zai yi jagoranci mai adalci da zai bunkasa rayuwar talakawa. Hakika Allah ya ba wa marigayi dammar yin shugabanci na wa’adi biyu tsawon shekaru 8 inda bayan sauka daga karaya da kimanin shekaru biyu da wata daya da kwanaki Allah ya karbi abun sa. Labari daga wajen dan uwan sa Malam Mamman Daura marigayin ya ma samu sauki kafin ciwon ya sauya kala inda hakana ya zama ajali. Ita cutar ajali wani loakcin ta na da irin wannan yanayi na mai jinya zai samu sauki har ma ya yi magana da dammar aikawa da sakonni ko yin wasiyya inda daga bisani sai ciwo ya dawo shikenan sai rai ya yi halin sa. A labarin da a ka samu ta hanyar matar sa Aisha, marigayin ya ba ta sakon ta bukaci ‘yan Najeriya su yafe ma sa gabanin a kai shi kabarin sa. Wanda ya yi mulkin kasa irin Najeriya kuma ga ma irin shugaban da a ke kyautatawa zato zai tabuka abun kirki ba zai zama abun mamaki ba a samu ra’ayoyi mabambanta game da shi. Abun da ya zama rinjaye shi ne akasarin jama’a na nuna juyayi kan rasuwar Janar Buhari kuma har ma da ambata cewa sun yafe ma sa laifukan da su ke ganin ya aikata mu su musamman ga rashin samun muradun da su ka sa ran samu lokacin da ya hau madafun iko. Ba mamaki lura da irin haka na samuwar wadanda su ka samu sanyin guiwa kan yanayin mulkin sa, marigayi Buhari ya fito ya nemi ahuwar su ya na mai tabbatar da cewa akwai wadanda zai yiwu ya mu su ba daidai ba don haka ya na neman su yi hakuri su yafe. Ga al’ummar arewacin Najeriya da dama marigayin ne gwanin su, da yawa sun shiga damuwa kan yanda gwamnatin ta sat a rufe kan iyaka da hakan ya dakatar da hada-hadar kawo kayan masarufi musamman abinci. Rashin shigowar abinci ya haddasa tashin farashin kayan abincin ba ma irin shinkafa. Lokacin da jama’a da dama ke korafi su kuwa manoma shinkafa farin ciki su ke yi don hanyar arzikin su ta bude. Marigayin ya ba da dalilin daukar matakin ne don a rika noma abinci a cikin gida. An noma abincin amma ba mamaki saboda rashin isar tallafin gwamnati ga harkar noman ya sa kayan da a ka noma su ka zama da dan karen tsada. Ga kasa gaba daya yanda a ka rika samun hauhawan farashin man fetur ya jawo damuwa ainun da jefa al’umma cikin kunci duk da ma ashe a lokacin ba a gama cire dukkan tallafin man ba kenan. A karshen mulkin sa gabanin zaben 2023 marigayi ya kawo wani tsari na canja kudi inda hakan ya kawo karancin takardun kudi a tsakanin jama’a. Wannan ya haddasa matsaloli da yawa kuma ba a samu sa’ida ba sai da kotun koli ta yanke hukunci kan amfani da sabbi da kuma tsoffin kudi. Bayan an farfado daga matsalar marigai Muhammadu Buhari ya baiyana cewa an dau matakin ne don hana ‘yan siyasa sayen kur’a a babban zabe. Shin ‘yan siyasar sun sayi kuri’ar ko hakan ya dakile su daga samun dammar saya don haddasa magudin zabe, an dai gudanar da zaben kuma jam’iyyar APC ta marigayin ta zarce da mulki karkashin shugaban da keg ado yanzu wato Bola Ahmed Tinubu. Sauran duk wani zance ko karafi ya zama tarihi. Haka manufofin gwamnati su ke ko sun yi wa ‘yan kasa dadi ko ba su yi ba zai hana gwamnatin daukar matakan da ta ke ganin su ne mafi a’ala ga kasa ba. Abun da talakawa su ka fi tsammani ga gwamnatin marigayin da su ke dauka gwamnatin su ce, in sun yi korafi ta saurara kuma ta biyewa bukatun su. Duk yanda mu ka dau lamarin gwamnati ya iya wuce tunanin mu. Mulki musamman a irin Najeriya tamkar kokwa inda na bayan fage a kan ce shi ne gwani don ba mamaki ya na ganin da an yi haka sai ka ga an samu nasara. Mu jama’ar kasa mu na waje mu na duba abubuwan da gwamnati ke yi kuma kalilan ne daga cikin mu ke da sahihan bayanan gaskiya na abun da ke faruwa ko dalilan da su kan kawo kwan gaba kwan baya. Wadanda su ka jajirce ga ba wa marigayi uzuri su ne wadanda ke cewa rashin lafiya ta hana shi yin mulki tamkar yanda a ka yi tsammani. Shi kuma marigayin kan nuna kamar ba mai yiwuwa ba ne ya tabuka yanda ya yi a mulkin soja don lokacin da kuruciya kuma ai soja kan yi aiki ne da dokar soja ba ya amfani da tsarin mulki. A dimokradiyya ya zama wajibi shugaba ya rika aiki da majalisar dokoki. Farkon mulkin Buhari an a za samun tafiyar hawainiya ga rashin jituwa tsakanin fadar gwamnati da majalisar dokoki karkashin sanata Bukola Saraki don yanayin yanda shugabancin majalisar ya zo ba tare da goyon baya ko amincewar sashen zartarwa ba. An yi ta matakai na neman tsige Saraki amma hakan ya ci tura har ya kamala jagorancin sa a 2019. Dagan an an samu majalisa da ta tafi da fadar gwamnati kusan 100/100 karkashin sanata Ahmed Lawan. ‘Yan Najeriya su ne shaida shin an samu nasarar cimma muradun gwamnatin talakawa ko kuwa a’a. Nan dai har marigayi ya samu ya kamala wa’adin say a mika ragama ga sabon shugaba Tinubu a ranar 29 ga Mayu 2023. An san dai babu batun tallafin man fetur a kasafin kudi na wannan shekarar amma tsohuwar gwamnati ta bi hanyoyi irin na ta hart a sauka ba ta kammala janye tallafin ba. Ilai kuwa a nan wajen karbar mulkin sabon shugaba Tinubu ya aiyana cewa tallafin man fetur ya tafi! Daga nan dai kowa ya san yanda kasar ta shiga inda farashin kayan masarufi ya kara cillawa sama. Gaskiyar magana talakawa sun kara shiga matsalar rayuwa amma in an duba duk manyan ‘yan takara na adawa ma sun yi alwashin cire tallafin in an zabe su. Bambancin da masu sharhi ke magana a kai shi ne shin janyewar a jawabin farko da shugaba Tinubu ya yi haka ma sauran za su iya yi ko sai an dan tafi kadan a rika janyewa a hankali har a kamala gaba daya? Koma yaya mu ka kalli wannan al’amari ya dace gwamnati ta dimokradiyya ta rika sara ta na duba bakin gatari don kar a a wayi gari kukan jama’ar kasa ya fi murmushin su yawa.
Marigayi shugaba Muhammadu Buhari dai ya tabbata cewa ya na da takatsantsan da dukiyar jama’a wato kai tsaye ba za a iya zargin sa da tara abun duniya ba amma ba mamaki wasu mukarraban sa sun hana nasarar wannan yanayi na rikon amana da kau da kai daga tara dukiya. An sha mamaki yanda hukumar yaki da cin hanci EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan babban banki Godwin Emefiele da zargi na mummunar badakala da ya aikata karkashin mulkin marigayi Buhari. Ta yiwu akwai wadanda a gwamnatin Buhari ke amfana da Emefiele da hakan ya sa ko bayan kamala wa’adin mulkin sa a ka sabunta ma sa wani wa’adin. Mafi mamakin ma gwamnatin ta gaje shi ne daga tsohuwar gwamnatin Goddluck Jonathan da ta zarga da badakala. Akwai wasu misalan da ke nuna Buhari dai ya zuba ido don dabi’ar wasu daga makusanta kan iya sabawa da akidar sa amma ba zai iya hukunta su ba don shekaru sun jab a kamar yanda ya ke a mulkin soja shi da marigayi Tunde Idiagbon ba.
KAMMALAWA
Duk mai rai mamaci ne don haka a kyautata harshe ga wanda Allah ya karba da yi ma sa fatar samun rahama daga Allah. Dukkan mu wataran hanyar daya ce. Allah ya sa mu gama da duniya lafiya. Daga dawowa mulkin Buhari bayan shekara 30 da barin madafun iko na soja shekara 10 ne cif hakanan ya kasance a tsawon shekaru 20 cikin dimokradiyya duk zabe akwai sunan marigayin kan katin kada kuri’a! yau kuma marigayi na gidan gaskiya da ke jiran duk mai rai!.
Nasiru Adamu El-hikaya