A halin da ake ciki, rundunar sojojin ukraine ta ce sojojinta sun janye daga garin Siversk na gabashin kasar a yayin da Rasha ta zafafa hare-hare kan garuruwa da birane masu muhimmanci ga kokarin Ukraine na kare gabashin kasar.
Faduwar wannan garin na Siversk yana zuwa ne a yayin da Ukraine take shan matsin lamba daga Amurka a kan ta yarda da yarjejeniyar zaman lafiya domin kawo karshen wannan yaki da aka yi shekaru hudu ana gwabzawa.
Kama wannan gari da Rasha ta yi, yanzu ya sa tazarar kilomita 30 kadai ta raba ta da wata muhimmiyar cibiyar, Sloviansk, dake yamma da nan.


