Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a laraba yace kasar bani yahudun, zata kashe kudi dala bilyan 110 cikin shekaru hudu masu zuwa, wajen kafa sashen kera makamai maizaman kansa domin kasar ta rage dogaro kan wasu kasashe wajen samun makamai.
“Zamu ci gaba da neman wasu muhimman bukatu, a hanu daya kuma zamu samar da makamai da kan mu, inji PM Netanyahu a lokacinda yake magana a bikin kaddamar da shirin.
Bana cewa kasa zata iya biyawa kanta bukatunta kachokam ba, amma zamu yi bakin kokarin mu waje ganin haka. “in ji shi.
Burin mu shine gina sashen kera makamai na kasar Isara’ila domin mu rage dogaro kan kasashe ciki harda kawayen mu.
A gefe daya kuma, Isra’ila ta fada a Laraban nan cewa, zata dauki fansa bayan da ta zargi Hamas da keta yarjejeniyar tsagaita wuta, bayanda wani sojanta ya sami rauni sakamakon wata fashewa a Gaza, sai dai hamas ta musanta zargin, tana mai cewa, fashewar daga wani makami ne da aka bari a wurin tun lokacinda ake bata kashi.
PM Netinyahu ya ma baci lamarin ne da ya auku a Rafah, inda Isra’ilan take daukar matakan soji a yayinda yake magana a wani bikin yaye daliban makarantar horasda sojojin sama na kasar, ya kara da cewa Hamas ta fito fili ta nuna cewa ba zata kwance damara ba, kamar yadda yake kunshe cikin yarjejeniyar da aka kulla na tsagaita wuta a cikin watan Oktoba.
A wani gefe kuma, yan share wuri zauna na Isra’ila a wani dan karamin wuri da ake kira Or Meir, sun bayyana a shafukan Telegram shirin su na ci gaba da korar Falasdinawa a yankin.


