Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Amurka Ta Sanya Hanu Kan Yarjejeniyar Kiwon Lafiya Da Ƙasashen Madagascar, Saliyo, Botswana, Ethiopia
Published: December 25, 2025 at 7:33 AM | By: Bala Hassan

Amurka ta sanya hanu kan sabbin yarjejeniyoyin kan kiwon lafiya da kasashen Madagascar, Saliyo, da Botswana, da kuma Ethiopia, wadda adadin kudaden da shirin zai bukata suka kai kusan dala bilyyan 2 da milyan 300, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fada a ranar talata.

A cikin watan Nuwambana bana ne gwamnatin shugaba Trump ta bayyana wani sabon tsarin tallafi gameda tallafin Amurka take bada wa ga kasashen ketare, da ya fi maida hankali wajen ganin kasashen da take taimakawa suna daukan hakkin kula da kiwon lafiyar kasashen su.

A cikin ko wace yarjejeniya ta kunshi sharudda da suka hada da aiwatar da ita sau da kafa, da kuma matakan ladabtarwa idan aka kaucewa yarjejeniyar, auna ci gaba da ake samu wajen ganin bayan barazana daga wasu cututtuka, da kuma kaucewa dogaro kan tallafin  da Amurka take bayarwa, kamar yadda ma’aiktar harkokin wajen Amurka ta fada a cikin wata sanarwa data fitar.

A duka yarjejeniyoyin Amurka ta kuduri anniyar zata kashe kudi dala bilyan daya da milyan dari hudu, yayinda kasashen hudu su  kuma za su kashe dala milyan dari tara daga aljehunansu.

Ofishin jakdancin Amurka dake Abidjan babban birnin kasar Ivory Coast ta ce sanya hanu kan yarjejeniyar kiwon lafiya na tsawon shekaru biyar da kasar, za’a gudanar da shi ranar Alhamis idan Allah ya kai mu.

Kamar yadda ofishin jakadancin ya ci gaba da cewa, yarjejeniyar an tsara ta ne da nufin karfafa hanyoyin gano bullar cututtuka da samar da ma’aikata, ta kara da cewa, Amurka zata samarda kudi dala milyan 273, Ivory coast kuma zata bada kudi bilyan 252 na kudin sefa.

Ahalinda ake ciki kuma, matakin janye jakadu masu yawa daga kasashen Afirka da suke kudu da hamadar sahara da Amurka tayi, zai bar Washington bata da manyan kwararru a kusan rabin kasashe da suke yankin, matakin da zai kara dagula yunkurin aiwatar da burin gwamnatin TRump a yankin da yake fama da juyin mulkin soja.

Tun fara aikin gwamnatin Trump, hukumomi a Washington suka bada karfi wajen gudanr da harkokin kasuwanci maimakon bada karfi kan tallafi.

Shugaba Trump ya maida karfi wajen ganin an cimma zaman lafiya, da kuma sanya hanu kan yarjejeniyin samarda muhmman albarkatun kasa, maimakon tallafi.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Netanyahu: Zamu Kashe Dala Billiyan $110 Cikin Shekaru Hudu Don Kera Makamai
Next Post: Mala Buni: Zai Jagoranci Kwamitin Sassanci Na Jam’iyar APC

Karin Labarai Masu Alaka

Dalibin Jami’a Ya Rasa Ransa A Birnin Dakar Yayin Zanga Zanga Afrika
Hukumomin Bada Agaji Sun Fadakar Da Al’ummar Jihar Gombe Afrika
Nada Jakadu Da Tinubu Yayi Sako Ne Ga ‘Yan-Arewa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Jami’an Tsaro Na Amfani Da Damar Su Wajen Cin Zarafin Jama’a Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai Afrika
Ribadu: Najeriya Ce Kasa Daya Tilo Da Ke Tabbatar Da Demokraɗiyya A Sahel Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Rasha Na Cigaba Da Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Ga Ukrain Labarai
  • Ansamu Girgizar Kasa A Kasar Taiwan Labarai
  • Nwakali Na Dab Da Komawa Kungiyar PAC Omonia Ta Cyprus Wasanni
  • Trump Zai Sasanta Tsakanin Masar Da Habasha Amurka
  • Rasha Da Ukraine Sun Cigaba Da Yakar Juna Afrika
  • Bahrain Ta Gabatar Da Kudurin Sulhu Ga MDD Afrika
  • Kasar Congo Ta Dau Alwashin Bin Tsari Wajen Rarraba Ma’adanai Afrika
  • Lawal, Filin Wasa Na Rashidi Yekini Ko Turai Iyaka Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.