Jamhuriyar Nijar ta sanar da ɗaukar matakin ramuwar gayya ta haramta bai wa ’yan ƙasar Amurka biza gaba ɗaya, tare da hana shigowar ’yan ƙasar Amurka ƙasar Nijar na dindindin.
Wannan mataki na diflomasiyya mai ƙarfi ne, wanda ke da manyan tasiri ga dangantakar yankin da kuma hulɗar ƙasa da ƙasa.
Hakan ya biyo bayan sanarwar da Amurka tayi na dena bawa yan kasar Nijar bizar shiga Amurka, don haka shugabannin Nijar suka dauki matakin hana Amurkawa Shiga kasarsu
Kamfanin dillancin labarai na ANP ya ruwaito wata majiyar diflomasiyya na cewa ƙarƙashin dokokin gwamnatin Nijar babu wani ɗan Amurka da za a sake baiwa visa ta kowacce hanya haka zalika an haramtawa Amurkawa sanya ƙafa a cikin Nijar da sunan kowacce irin ziyara.
Majiyar diflomasiyyar ta ce mahukutan ƙasar ta Nijar ta umarci ma’aikatar harkokin wajen ƙasar da kada ta sake bayar da visa ga Amurkawa, matakin da ke nuna haramci na dindindin.
Majiyar ta bayyanawa kamfanin dillancin labarai na ANP cewa matakin na nuna cewa bazata duƙa ba, haka zalika ba zata zuba ido ga hukuncin na Amurka ba, maimakon haka za ta ɗauki mataki daidai da wanda Washington ta ɗauka.
A ranar 16 ga watan Disamba ne, Washington ta ƙara ƙasashe 7 ciki har da jamhuriyyar Nijar a jerin ƙasashen da za su fuskanci haramcin samun izinin shiga Amurka.


