Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa, ya halarci wurin gwajin wasu makamai masu linzami masu cin dogon zango da kasar ta gudanar a ranar lahadi.
Kamfanin Dillancin labarai na kasar yace shugaba Kim ya bayyana cikakkiyar gamsuwarsa, a yayin da wadannan makamai masu linzami suka tashi suka bi ta inda aka auna su, kuma suka far ma inda aka yi niyya cikin teku a yamma da yankin kasar ta Koriya.
Kim ya jaddada cewa Koriya ta Arewa zata ci gaba da maida hankali kacokan wajen ingantawa da bunkasa makaman nukiliya.
Rundunar sojojin Koriya ta Kudu ta fada ranar litinin cewa dakarunta sun gano harba makamai masu linzami da aka yi da misalin karfe 8 na safiyar ranar lahadi daga yankin Sunan a kusa da Pyongyang, babban birnin Arewa.
Kamfanin dillancin labaran Yonhap na Koriya ta Kudu yace tana yiwuwa Koriya ta Arewa ta gudanar da wasu sabbin gwaje gwajen makamai masu linzami a daidai lokacin bukukuwan sabuwar shekara.


