
A karshe dai majalisar zartarwa ta Najeriya ta shirya don rantsar da shaharerren lauyan nan Barista Mainasara Kogo Umar a matsayin shugaban kotun da’ar ma’aikata.
Rantsarwar bias sanarwa za ta gudana a taron majalisar zartarwa a alhamis din nan a fadar Aso Rock.
In za a tuna shugaba Tinubu ya nada Barisra Mainasara a watannin baya amma a ka samu tsaikon fara aikin sa don yanda tsohon shugaban kotun Danladi Umar ya cigaba da zama kan kujera bisa bayanan rashin kammalar wa’adi.
Hatta majalisar dokokin taraiya ta shigo batun amma a ka yi ta samun kiki-kaka har dai kammaluwar wannan kalubalen.
Mainasara Kogo da ya yi matukar shahara musamman a kafafen labarum labaru, masanin kundin tsarin mulki ne na kimanin kasashe 7.