A Najeriya batun kwaskwarimar dokar haraji da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kudiri aniyar yi ne ke ci gaba da daukar hankalin ‘yan kasar.
A tsarin sabuwar dokar dai akwai batun kara yawan kudin da za’a cire a cikin asusun ajiya na Banki ga kowane dan kasar, lamarin da masana tattalin arziki sukace tabbas da sake.
Bayanai dai sun nuna yanzu ‘yan Najeriya na ci gaba da nuna yatsa ga ‘yan Majalisun su tare da yi musu kashedi na kar suyi kuskuren sanya hannu a wannan dokar.
Alh. Kabiru Abubakar Mai Jama’a mai sharhi kana masanin tattalin arziki, yana mai cewar akwai fargaba bisa la’akari da wani tsari na yanayin cinikayya a cikin sabbin tsarin harajin.
Shi kuwa Hon. Audu Buba dan Majalisar wakilan mai wakiltar Mazabar Chanchaga a Jihar Neja, a karkashin Inuwar Jam’iyyar PDP yana ganin ‘yan kasa suna da damar yin korafi akan wannan batu. Don kuwa duk wakili yana amsa sakon jama’ar shi ne.


