Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Adamu: “Yakar Cin Hanci Daga Tushe Itace Mafita Daya Tilo”
Published: January 2, 2026 at 2:35 PM | By: Yusuf Aliyu Harande

Hukumar yaki da cin hanci ta ICPC ta hada kai da jihohi don karfafa tasirin yaki da cin hanci daga tushe.

A taron wuni daya a Abuja, ICPC ta ce hakika kwamishinonin shari’a na jihohi na da gagarumar rawar takawa a yaki da almundaha.

Taron wanda ya samu halartar ministan shari’a Lateef Fagbemi da tsohon minista Kanu Agabi  ya ja hankalin kwamishinonin da cewa lallai gwamnoni na sauraron shawarar su don haka ya dace su yi amfani da damar wajen kawo gyara.

Shugaban hukumar ta ICPC Barista Musa Adamu ya ce nadama kan biyo bayan duk jami’in da ke da alhakin gyara amma ya yi kasa a guiwa “lokacin da mu ka bar kujera ko tsufa ya same mu za mu ga abubuwan da ya dace mu yi to in kuwa ba mu yi ba tarihi ba zai yafe ma na ba.”

Kwamishinan shari’a na jihar Yobe Barista Saleh Samanja ya ce yaki da cin hanci kan samu nasara ne ba a lokaci daya ba don haka za a cimma nasara ta hanyar jajircewa.

Hakanan shi ma kwamishinan shari’a na jihar Jigawa Barista Bello Abdulkadir Fanini ya ce aikin na kwamishinonin ya na da muhimmaci wajen saita yaki da rashawa a matakin na jiha kasancewar su masana lamuran shari’a.

Hukumar ta ICPC da kan yaki cin hanci a tsakanin jami’an gwamnati, ta yi alwashin sakamakon taron ba zai zama zane kan ruwa ba.

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/01/ICPC-COLLABORATES-WITH-STATES-ATTORNEYS.mp3
Labarai

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Sanda A Finland Sun Kwace Jirgin Ruwan Kasar Rasha
Next Post: NUJ: Akwai Bukatar Inganta Albashin ‘Yan Jarida A Najeriya

Karin Labarai Masu Alaka

Habasha Tafara Gina Filin Jirgin Sama Mafi Girma A Afirka Afrika
Meyasa Israela Take Hana Kaiwa Gaza Kayan Tallafi Afrika
Rasha Ta Yiwa Amurka Tayin Daina Bada Bayanan Sirri Afrika
Iran Tace Farisa Zata Kai Hari Kan Mayakan Amurka Amurka
Hukumar ICPC Ta Gayyaci Dangote Labarai
Kasashen Faransa Da Italiya Sun Nuna Rashin Amincewa Da Matakan Sojoji Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sojin Najeriya Da Amurka Sun Hallaka Jagoran ISIS Afrika
  • Kungiyar Kwallon Mata Sun Tsallaka Iyakar Turkiyya Zuwa Iran Afrika
  • Kotu A Najeriya Ta Kame Mutane Bisa Zargin Ta’addaci Afrika
  • Wike: Bazamuyi Sake Fubara Ya Sake Samun Nasara Ba Najeriya
  • ‘Yan Sandan Habasha Sun Kama Dubban Albarusai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Rasha Ta Nuna Kudurin Cimma Zaman Lafiya Da Ukraine Amurka
  • Ferfesa Pantami Yasamu Tikitin Takarar Gwamnan Gombe A Jami’yar PDP Afrika
  • Shugaba Tinubu Ya Yayi Magana Game Da Kafa ‘Yan Sandan Jihohi Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.