An yi girgizar kasa me Karfin gaske a kudancin kasar Mexico ranar Jumu’a da safe, inda ta lalata tituna da asibitoci, kuma ta kawo dan jinkiri ga jawabin shugaba Claudia Sheinbaum a Taron Manema labarai na farko a wannan shekarar.
Wata mata me shekaru 50 ta rasu a jihar Guerrero da ke kudu maso gabashin kasar, lokacin da gidan ta ya fadi saboda girgizar, a cewar gwamnan jihar Evelyn Salgado kuma kafar yada labarai ta kasar ta ce wani mutum mai shekaru 67 ma ya rasa ran sa a birnin Mexico yayin da yake kokarin sau kowa daga bene don tserewa daga gidan shi.
Lokacin da girgizar kasar ta auku, a babban birnin kasar, wani babban gini me tsawon mita 45 da aka yi don tunawa da ranar samun ‘yancin kasar a wani babban shataletale, da ke da nisan mil 180 daga inda girgizar ta auku sai da ya rika kadawa hagu da dama.


