Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kai farmaki wajen hakar ma’adanin gwal na Morila a kasar Mali karshen makon da ya wuce, inda suka kona kayayyakin aikin, kuma suka yi garkuwa da ma’aikatan gurin guda bakwai, kamar yadda wani jami’i a ma’aikatar ma’adanai ta kasar ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters ranar Litinin.
Wannan harin yana nuni da kara tabarbarewar tsaro a Mali, wadda ita ce kasa ta uku da ta fi samar da gwal a Afirka, da ke yaki da ‘yan ta’adda da ke da alaka da kungiyar Al-Qaida, wadanda kan kai farmaki ga kadarori na tattalin arzikin kasa, da kayan zuba jari a kasashen waje.
Mutane dauke da makamai, sun kai farmaki inda aka hakar ma’adanin, wanda wani kamfanin kasar Amurka, Flagship Gold ya rattaba hannu kan yarjejeniyar kasuwanci a shekarar da ta gabata, a cewar wani me magana da yawun ma’aikatar hakar ma’adanai ta kasar Mali.
Wani da ke da masaniya a kan abun ya kara da cewa, sun kokkona kayayyakin aiki, sannan suka yi garkuwa da ma’aikata bakwai, amma duk sun sako su washegari da yamma.


