Shugaban Kungiyar ‘yan Jarida a Najeriya Kwamrade Alhassan Yahya Abdullahi ya bayyana bukatar dake akwai na samar da inshorar lafiya data Rayuwar ‘yan jarida a fadin ƙasar.
Shugaban ya bayyana hakane lokacin da Yake shaida bada tallafin Kudade ga iyalen ‘yan jarida bakwai da suka Rasa Rayukansu a hatsarin mota a makon daya gabata a Gombe.
Wakilin GTA Hausa Amurka Ke Magana a Gombe, Aliyu Bala Gerengi Yana dauke da cikekken rahoto.


