Gwamnatin Amurka ta tabbatar da ƙwace wani jirgin dakon man fetur da ke ɗauke da tutar ƙasar Rasha, bisa zargin karya dokokin takunkumin da aka kakabawa Moscow.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaron ruwan Amurka ne suka mamaye jirgin a cikin teku, inda suka karbe iko da shi bisa zargin yana jigilar danyen mai ba bisa ka’ida ba zuwa wasu ƙasashe.
Wannan mataki na zuwa ne a wani lokacin da ake ci gaba da takaddama tsakanin kasashen yamma da Rasha, musamman sakamakon yakin Ukraine, wanda ya jawo takunkumi da dama daga Amurka da ƙawayenta akan Rasha.
Hukumomin Amurka sun ce za su ci gaba da sa ido da aiwatar da dokokin takunkumi domin hana Rasha samun kudaden shiga daga fitar da danyen mai.
Haka zalika, gwamnatin Rasha ba ta yi wata sanarwar kai tsaye ba kan lamarin, amma wasu jami’ai sun bayyana cewa wannan mataki na Amurka zai kara dagula alakar diflomasiyya tsakanin bangarorin biyu.


