Shugabar ‘yan hamayya a Venezuela, Maria Corina Machado, ta gana da Paparoma Leo a fadar Vatican a ranar Litinin, inda daga bisani tace ta roki Paparoma ya sa baki domin hukumomin kasar a Caracas su saki fursinonin siyasa.
Fadar Vatican ta tabbatar da ganawar kamar yadda bayanai da take baiwa ga manema labarai ako wace rana suka nuna a jiya litinin din, sai dai fadar bata yi wani karin bayani ba.
A cikin wani gajeren video da fadar Vatican din ta bayar, an ga shi Paparoman da Maria suna gaisawa da murmushi, zaune suna fuskantar juna a teburin Paparoma a babban ofishinsa.
Ahalinda ake ciki kuma, ranar Alhamis ake sa ran Maria Machado zata gana da shugaban Amurka Donald Trump, kamar yadda wani jami’i a fadar White House ya fada ranar Litinin.
Ita kuma shugabar kasar Mexico Claudia Sheinbaum tace Amurka ba zata dauki matakin soja kan kasar ta ba a kokarin Washinghton na yaki da safarar miyagun kwayoyi, bayan wata tattaunawa mai “gamsarwa,” da tace tayi da shugaba Trump a jiya Litinin.


